Musa Iliyasu na shirin rusa Jam’iyyar APC a Madobi – Daga Usman Sarki

A wannan karon ma tarihi yana neman maimaita kansa a wata sabuwar siga da amfani da sunan Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje wajen jaza masa baqin jini don cimma manufar wani mutum daya tilo wanda ko a zaben daya gabata baiyi tasiri ba wajen cin zaben APC a Karamar hukumar Madobi duk da kororotonsa da kallon dayake wa kansa a matsayin jagora a Karamar hukumar Madobi...

0

Karamar hukumar Madobi ta kasance daya daga cikin kananan hukumomi da ke da tsarin siyasa na ra’ayin kansu tare da tsantsar rashin amincewa da tsarin qaqaben yan takarkaru a matakai daban daban yayin gudanar da zabubbuka. A shekara ta 2017 an gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Kano inda Jamiyya mai mulki ta APC ta kame dukkan kujerun shugabanni da kansiloli a fadin Jihar baki daya. A wancan lokaci an lullube kura da fatar akuya inda aka gabatar da mutumin da ya fito daga wata Karamar hukumar (Tarauni) akayi amfani da sunan Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje wajen hana dimokaradiyya tayi aikinta wajen tsayar da sahihin Dan takara inda aka tsayar da Dan Karamar hukumar Tarauni ya zamo shugaban Karamar hukumarmu ta Madobi. Wannan shine rashin adalci mafi girma da aka yiwa al’ummar Karamar hukumar Madobi wanda munyi kiraye kiraye ga Gwamnati da Jam’iyyar APC akan ayi duba kan wannan al’amari amma hakan bata samu ba.

A wannan karon ma tarihi yana neman maimaita kansa a wata sabuwar siga da amfani da sunan Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje wajen jaza masa baqin jini don cimma manufar wani mutum daya tilo wanda ko a zaben daya gabata baiyi tasiri ba wajen cin zaben APC a Karamar hukumar Madobi duk da kororotonsa da kallon dayake wa kansa a matsayin jagora a Karamar hukumar Madobi.

READ  The Importance of Educating Girls

A wannan gaba inaso inyi kira da kakkausar murya ga Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Jam’iyyar APC akan irin kisan mummuqen da kwamishinan raya karkara Honourable Musa Iliyasu Kwankwaso ke yiwa Gwamnati da Jam’iyyar APC a Karamar hukumar Madobi ta hanyar sake maimaita kuskuren da aka aikata a baya na qaqaba mana Dan Karamar Hukumar Tarauni a matsayin Dan takara wanda zai sake mulkar Karamar hukumar Madobi a matsayin shugaba da sunan cewa umarni ne daga Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Hakika mu al’ummar Karamar hukumar Madobi mun tabbatar da matsayar Mai Girma Gwamna itace ayi komai bisa doka da tsarin dimokaradiyya wanda wannan tsari bai bada damar tsayar da mutumin daya fito daga wata Karamar hukuma takara a Karamar hukumar da ba tasa ba. Yin sahihin zaben fitar da yantakara bisa gaskiya da adalci shine zai bada damar mutanen Karamar Hukumar Madobi su zabi dan su domin ya mulke su ba dore ba. Naka shi yasan matalolin ka kuma shine zai share hawayen talakawa masu zabe ba biyan bukatun wasu tsiraru da suke yawo suna rawa da bazar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba.

READ  Wakilcin Kura/Madobi/Garun Malam: Bata Sake Zani ba - Daga Usman Sarki

Amfanin mulkin dimokaradiyya shine tafiya da zabin jama’a wanda shine zai kaisu ga tudun muntsira ba dauki dora ba da zata bar baya da kura. Hakika kurar qaqaba mana Dan Tarauni bata kwanta ba sai gashi za’a kara tayar da ita. Duk Shugaban da ya damu da al’umma zabin su shine na shi, amma idan aka sanya kasuwar bukatun kai sai ayi kama karya a karya inda babu gaba su ba damuwar su ce ba.

A bisa wannan nake sake kira ga yan kwamitin kokas da sauran masu ruwa da tsaki na Karamar hukumar Madobi da su tuna da amana da nauyin da Allah ya dora musu na tabbatar da adalci wajen tsayar da yan takarkaru a dukkan matakan da za’ayi zabe akansu. Ya zama wajibi in sake yin kira ga shugabannin Jam’iyyar APC na Karamar hukumar Madobi da Dan Majalisar Jiha mai wakiltar Karamar hukumar Madobi tare da sauran yan takarkarun da suka fito daga Karamar hukumar Madobi da su tuna da cewar sune suka bada gudummawa tare da mu al’ummar Karamar hukumar Madobi wajen tabbatuwar nasara Jam’iyyar APC a zaben 2019 lokacin Honourable Musa Iliyasu Kwankwaso yana gidan radio yana bada labarin ‘JABBAL QALAM’.

READ  One century After: Throne Returns to Bamalli’s ruling House

Ina kara kira ga Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Jam’iyyar APC da su sake bincike akan agendar Honourable Musa Iliyasu Kwankwaso da Alhaji Lawan Yahaya musamman ta hanyar yin waiwaye ga zaben 2019 tare da komawa dayin duba na tsanake ga sunayen shugabannin kananan hukumomin da akayi amfani dasu wajen kifar da Gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda yayi sanadiyyar zaben inconclusive.

Usman Suleiman Sarki Madobi
sarkiusmansuleiman@gmail.com

Leave a Reply