Matasa Sune Mafi Dacewa da Jan Ragamar Shugabanci a Najeriya – Daga Usman Sarki

Babban abu na farko dayake tasiri shine lafiya da karfi na jagororin al'umma. Idan mukayi duba zamuga mafi yawanci kasashe a yanzu sun hutar da dattawa tare da janye su daga madafun ikonsu tare da maye gurbinsu da matasa a fagen shugabancin al'umma.......

0

Tafiyar da harkoki da al’amuran al’umma da kasa baki daya suna bukatar abubuwa da yawa domin kaiwa ga cimma nasarorin da zasu ciyar da kasa gaba.

Babban abu na farko dayake tasiri shine lafiya da karfi na jagororin al’umma. Idan mukayi duba zamuga mafi yawanci kasashe a yanzu sun hutar da dattawa tare da janye su daga madafun ikonsu tare da maye gurbinsu da matasa a fagen shugabancin al’umma.

Idan mukayi duba ga shugabannin da suka taka muhimmiyar rawa anan Nigeria da sauran kasashen Afirka zamuga mafiyawancinsu sunyi mulki ne suna matasa masu cikakkiyar lafiya ta jiki ga kuma karfi ta yadda suka duqufa wajen aiki ba tare da gajiyawa ba wajen jajircewa su saka kasashen su akan turba ta gari. Alal misali anan Najeriya Janar Yakubu Gawon, Marigayi Janar Murtala Ramat Muhammed, Marigayi Captain Thomas Sankara da Janar Muhammadu Buhari da sauransu duk sun taka rawar gani a lokacin da sukayi mulki suna matasa inda suka taka rawar gani wajen tafiyar da mulki. Amma yanzu kasancewar Shugaban Kasa Buhari shekarun sa sun ja takai ga har mutane suna tababa akan shine ko ba shine ba. Wannan yana nuni da cewa akwai buqatar ayi duba cikin matasa domin a basu damar taka rawar su wajen gina kasa da tabbatar da ingantaccen tsaro.

READ  Three Days Principles of Life - By Usman Suleiman Sarki

Abu na biyu matasa jagorori suna kokarin sauraron koke koken al’umma domin akwai wadanda zasu iya tsawatar musu idan sukayi ba daidai ba ko kuma jama’a suka koka to cikin sauki da gaggawa suke sauraro su kumayi gyara inda ya dace sabanin dattawan dake rike da madafun iko da zasu ja bakin su suyi shiru har sai an rasa bakin zaren a kare da ba mutane hakuri.

Abu na uku, matasa babu abunda ke gaban su banda tsara wata manufofi da zasuyi aiki dasu domin cimma nasarori domin subar kyawawan abubuwan koyi wanda idan rayuwar tayi tsawo za’a rinka gani tare da alfahari da irin namijin kokarin da sukayi a wajen kawo sauyi.

READ  Buhari Administration fails - By Ibrahim Birnin Kudu

Abu na hudu, matasa sune ke kokarin nada abokan aikin domin farawa mutane aiki ba sai wuri ya qure ba. Mai karatu zai yarda dani cewa lokacin da wannan gwamnati tazo a zangon farko saida akayi wata shida ba’a nada ministoci ba sabanin yadda muka gani a Faransa inda shugaba Emmanuel Macron wanda ana rantsar a kasa da kwana uku ya nada ministocin sa. Amma jinkirin da akayi wajen nada ministoci a Nijeriya a zangon farko na wannan gwamnati kwalliya bata biya kudin sabulu ba musamman anan arewa da muke tunanin mun hau jirgin ceto.

Abu na biyar shine matasa sune zasu dubi tafiyar gwamnatin su suga inda ya dace suyi gyara domin gane mai kwazo. A zangon farko na wannan gwamnati har ta gama babu ministan da akayiwa canjin aiki duk da cewa idan aka tsefe ayyukan da sukayi basu taka wata rawar gani ba da har talakawa zasuyi alfahari da tutiya da wannan gwamnati.

READ  Shin kun san yadda ake wankan tsarki ?

Idan muka lura duk harka bata tafiya daidai sai an hada da matasa idan ko aka tara taro dattawa to tabbas bazasu iya jajircewa ba saboda rauninsu musamman a fannin lafiya da karfin juriyar aiki. Saboda haka ya zama wajibi muyi karatun ta nutsu mu hutar da dattawa sai dai su bada shawara ba mika masu ragamar da ba zasu iya rikewa ba in ko ba haka ba zamuci gaba da maida hannun agogo baya.

Allah ya taimaki kasarmu ya azurtamu da shugabanni masu kwazo da kishin kasa.

Usman Suleiman Sarki
08058330007
sarkiusmansuleiman@gmail.com

Leave a Reply