Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Sunusi Lamido Sunusi ||

Allah SWT ya azurtaka da lafiya kuma ya inganta lafiyar sannan ya baka damar yin amfani da ita wajen bauta masa da sauran al'amuran yau da kullum...

0

Assalam alaikum warahmatullahi Ta’ala wa barakatuhu ! Bayan sallama irin ta addinin musulunci, zan fara da jajanta maka bisa qaddarar da ubangiji ya jarabceka da ita tare da yin addua’ar Allah ya baka ikon dangana da kuma cin wannan jarrabawa.

Bayan haka, na rubuta wannan takarda ne a matsayina na Dan uwanka musulmi kuma dan asalin jihar Kano domin tunatar dakai tare da baka shawarwari domin kyautatuwar zamantakewa da dumbin al’umma da ake muamala dasu. Hakika Allah SWT ya azurtaka da abubuwa guda hudu da zasu iya zame maka mafita duniya da qiyama amma abin mamaki da ban tsoro shine yadda ake neman barin wadannan baiwa da ubangiji ya bayar sun wuce ba tare da an ribace su. Wadannan abubuwan guda hudu sune:

  1. Lafiya
  2. Ilimi
  3. Dukiya
  4. Mulki

Allah SWT ya azurtaka da lafiya kuma ya inganta lafiyar sannan ya baka damar yin amfani da ita wajen bauta masa da sauran al’amuran yau da kullum.

Al’umma sun shaida cewa Allah SWT ya azurtaka da ilimi na addini dana zamani wanda sune fitilar dake haskaka tsarin rayuwar Dan Adam a duniya da qiyama baki daya. Hakan na tabbatuwa ne yayin da mutum ya kasance mai aiki da iliminsa a koda yaushe kuma a aikace bawai a furuci ba.

READ  #NorthernLivesMatters: The Voices of True Activists must be heard

Idan muka dubi bangaren dukiya, Allah azurtaka da dukiya wadatacciya domin kafi karfin duk wani abu da kudi keyi a fadin duniya.

A tsarin na mulki ka kai maqura domin Allah ya azurtaka da riqe matakai iri iri masu daraja matuqa kuma mafi girma shine Sarautar Kano a matsayin Sarki mai daraja ta daya.

Abin tsoro a tattare da duk wannan baiwa da Allah SWT ya azurtaka dasu shine yadda ka bari lokaci ke ja baka amfanesu ba domin a matsayinka na mai ilimi ya dace ace ka assasashi cikin al’ummarka ta hanyar fito da tsare tsare da zasu taimaka wajen ilmantuwar al’ummarka. Bugu da kari a matsayinka na mai dukiya, Allah ya bude maka Kofa ne wacce zaka shiga cikin dawwamammiyar rahamarsa amma idan kayi amfani da dukiyar wajen tallafawa al’umma wajen basu ilimi, samar musu da sana’oi ko basu tallafi domin samun sassaucin quncin rayuwa kamar yadda Mai Martaba Sarkin Gombe keyi a tsarin mulkinsa. Ka kasance mai kururuwa wajen bayyana irin halin talauci da rashin yin karatu tsakanin al’ummar arewacin Nigeria wanda shine bangaren daka fito amma a tarihi babu wani tsari na samar da ayyuka ga al’umma ko basu tallafin sana’a ko tallafawa makarantu ko dalibai daka assasa duk da manyan matakai na muqamai daka riqe. Duk da wannan kururuwa daka dinga yi babu wani lokaci da za’a kawo cikin tarihinka da za’ace ka kawo wasu qungiyoyi ko wata hukuma ta duniya data tallafa a wadannan bangarori, hatta makarantun dake cikin gidan Sarautar Kano basu zama daban sauran makarantu ba duk da kasancewar masanin ilimi da matsalolinsa a arewa.

READ  The NCDC Text Messages: Local Languages should be Inclusive

Kana cikin jerin masu mulki kuma mai sane da cewa mulki na Allah ne kuma shike bayarwa ga wanda yaso, ya karbe daga wanda yaso a lokacin da yaso, amma hakan bai hanaka jayayya da wannan iko na Ubangiji ba duba da rufe ido tare da adawa kakkausa da abokan aikinka Sarakuna Masu Daraja ta daya da Allah ya kawo kuma ya basu wannan mulki cikin ikon dayake dashi na yin hakan duk da kasan yin hakan tamkar fada ne da Ubangiji.

READ  Gaya Congratulates Ganduje on Supreme Court Victory

A bisa wadannan abubuwane nake bada shawarwari kamar haka:

  1. Ka kasance mai ilmantar da al’umma ta hanyar bada ilimin a aikace domin ya zama abin koyi ga masu koyon.
  2. Ka ware wani abu cikin dukiyarka don tallafawa al’umma mussamman mabuqata ta haryar ciyarwa, tallafin ilimi, sana’a da hidimtawa addini.
  3. Ka zama mai girmama dukkan hukuncin ubangiji musamman wajen yadda tare girmama duk wani wanda Allah yayiwa baiwar samun ilimi, dukiya ko mulki domin yin hakan wajibi saboda umarni ne ba ubangiji.
  4. Ka riqe zumunci da zama mai yafiya ga bayin Allah domin ka samu rabo mai girma a ranar lahira.

Wadannan dabiu ne da halaye na iyaye da kakanni daka gada kuma ya dace kayi koyi dasu.

A karshe ina yi maka fatan alkhairi da cigaba da samun kariyar ubangiji a koda yaushe.

Nagode.

Usman Suleiman Sarki
sarkiusmansuleiman@gmail.com
08058330007

Leave a Reply