Wani dan majalisar dokokin Najeriya ya ce an kashe akalla mutum 50 a harin da ‘yan bindiga suka kai kan wasu kauyuka a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar.

Hukumomi sun tabbatar da kai hari a garin a Kerawa na karamar hukumar Igabi ama basu tabbatar da adadin mutanen da aka kashe ba.

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Igabi, Zayyad Ibrahim, ya bayyana wa BBC cewa maharan su sama da 100 sun dirar wa garin Kerawa da wasu makwabtan kauyuka inda suka kashe mutane suka kuma kona gidaje da motoci.

READ  Shugabancin Buhari Yafi Cutar Corona Illa ga Al'ummar Najeriya- Daga Sarki

Zayyad Ibrahim ya kara da cewa maharan sun shiga kauyukan ne bayan an kammala sallar Asuba ranar Lahadi.

Ya kuma jaddada cewa adadin wadanda suka mutu zai iya zarta 50, yayin da wasu ke jinya a asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

READ  Zullum ya raba kayan tallafi wa ' yan gudun hijira

Dan majalisar ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo musu dauki ta hanyar kawo karshen kashe-kashen da ake fama da su.

Jihar Kaduna na cikin jihohi na baya bayan nan a Najeriya da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da kuma satar mutane domin neman kudin fansa.

READ  Karan kwana: sanyi ya yi ajalin wasu abokai 2 a Jos

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da kai mummunan harin.

Mai magana da yawun rundunar, ASP Mohamed Jalige, wanda ya tabbatar da kai harin, ya shaida wa BBC cewa yana jiran samun sahihan bayanai daga jami’ansu da ke karamar hukumar da aka kai harin kafin ya yi wani karin bayani.

Leave a Reply