Daga Comr. Abdullahi Muhammad Sagir

Kamar yadda Mallam yake kokarin samarda da dokar da zata yakaita amfani da luyukan waya sama da uku, akan kamfanonin sadarwan da suke Nigeria, kamarsu MTN, Airtel, Glo, 9mobile da sauransu.

Ina son Mallam ya bada umarnin kirkiran manhajar da zata taimaka wajen rigister layi wanda take dauke da bayanan BVN da kuma lambar shaidan katin dan kasa ( NIN Number ).

Muddin mutum bashi da wadannan abubuwan to bazai Budaddariyar Wasika zuwa ga Ministan Sadarwa, Pantami rijistan layi ba ko kuma sabun tashi.

Sannan manhajar zata iya zama kamar na hukumar Just, wanda da zarar kazo rijista ba’a bukatan bayannan ka kawai mutum zai dangwala dan yatsan sa ( Thumprints ) ne kawai sai bayannansa su fito daganan kawai sai a sabunta masa hoto kawai an kama masa rijistan layinsa.

Bayanan layukan mutum zasu zaunane akan BVN ko kuma NIN dinsa da zarar ya mallaki layi uku wani karin SIM bazai wuceba.

READ  Shin wani abu ne zakayi a gaban surukan kaji kunya ?

Duk mutumin aake bukatar wani nau’in layi na wani kamfani sai yaje yayi ‘mobile portability’.

Asa dokar ‘ Mobile Data’ ya zama maras iyaka ( unlimited access ) wato kamar yadda kamfanonin satellite sukeyi na wata-wata. Hakan zai samar da saukin amfani wa daliban kimiya da fasaha wajen gudanar bincike mai zurfi da kirkiran abubuwan ci gaba.

Sannan kowa a sama-masa wani lambar sirri ( Secret Code ) wanda zai mallaka shi kadai da zarar wayarsa ta bata ko an sace zai dannan wannan code na ‘USSD’ a wata wayar hakan zai bashi daman kulle layunka sa saboda bashi kariya kar’a aika laifi dashi ya shafeshi.

Inason Mallam ya tursasa kamfnonin sadarwa dasu takaita talluka na dole da suke sawa akan layukan mutane ba tare da saninsu ba saboda ba kowani dan Nijeriya bane mai ilmin fasaha kona turanciba.

READ  Sojojin Najeriya na Shirin kai farmaki Katsina don kakkabe 'Yan ta Adda

Sannan ina bukatan Mallam ya tursasa kamfanonin sadarwan na kasa dasu inganta sashen kula da abokan cinikaiya wajen canja tsarin ( customer care) hakan zai samarwa sauken korafi a dauki wayarka nan take da zarar ka kirasu a waya zasu dauka.


Da kuma samar da offisoshin tafi da gidan ka akoni yanki da akalla yakunshi masu amfani da layukan sadarwan mutum dubu biyu (2000).

Sannan Gwannati tayi kokarin dawo da Mtel da Nitel domin samun kudin shiga.

Hakan zai samar da abubuwa yi masu yawa wa ‘yan kasa.

Sannan zai samar da biliyoyin nairori wa gwamnatin Nijeriya za’a samu karin kudaden shiga da za’ayi wasu ayyuka dasu.

Zai kara samar da saukin rayuwa wa ‘yan Nijeriya.

Zai kara samar da tsaro wa Nijeriya, idan aka dauki wannan shawara tawa ta yin rijistan layi.

READ  TETFUND ta kaddamar da ayyukan N4.9bn a cikin ATBU Bauchi

Dolene kamfanonin sadarwan Nijeriya su samar da rubun adana bayanai ( Data Base) wanda jami’an tsaro da za su yi amfani da dashi wajen aiyukansu basai sun tuntube kamfanonin Sadarwa wajen Basu bayanaiba.

Ya zama wajibi gwannatin tarayya ta kara tauraron Dan Adam wajen cigaban ‘yan Nijeriya da kuma harkar tsaro, duba da eanda muke dashi basu wuce ‘yan kadanba, misali American da Rasha suna da akallah sama da dari bibbiyu muma muma mun kai mu yi da su saboda munada karfin tattalin arziki da zamu ita.

Daga karshe danso Mallam ya bani minti 30 in zauna da shi domin shawarwari suna da yawa sosai.

Naku , Comr. Abdullahi Muhammad Sagir 09031777225, 09030000490

Leave a Reply