Mafitar Nigeria Buhari ya sauka – Sheikh Gumi

0

A lokacin da al’ummar ƙasar nan musamman ma ‘yan yankin arewa suke ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cigaba da zarcewa akan mulki, a ganin da suke shi kadai mutumin da zai iya kai kasar tudun mun tsira.

Sheikh Dakta Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, har yanzu yana nan akan bakan sa na adawa da shugaban kasa Buhari.

Yana nan daram akan kalubalantar shugaban kasar duk kuwa da zagin da ‘yan Najeriya suke yi masa akan maganganun da yake kan shugaban kasar.

Duk abubuwan da Sheikh Gumi ya fada a baya akan abinda yake ji a jikin shi game da Buhari da kuma matsalolin da za a samu idan ya karbi mulki duka sun wuce yanzu.

READ  Tsokaci: Ziyarar gwamna tambuwal fadar shugaban kasa---Mal.Yasir Ramadan Gwale

Cikin wata hira da yayi da wakilan jaridar yanar gizo ta Desert Herald, Usman Ahmad da kuma Maryam Musa.

Malamin ya ce, yayin da Najeriya ke faman fuskantar matsaloli tun kafin yanzu dama shi can hankalinshi bai kwanta da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, kuma shine ya jawo duk abubuwan da suke faruwa a kasar nan yanzu irin su; matsalar tsaro, talauci, rashin aikin yi da kuma kara samun wasu kananan matsaloli na ta’addanci da suka hada da garkuwa da mutane da ta’addanci.

READ  Barazanar Yajin Aiki - Daga Ibrahim Birnin Kudu

Abinda, Janar Babagana Monguno ya fada a makon da ya gataba, wajen Sheikh Gumi, shine ummul aba’isin da ya sanya aka kasa kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan, duk kuwa da alkawuran da ya daukawa al’ummar ƙasar nan.

Sheikh Gumi ya ce ya zama tilas shugaban kasar ya kawo karshen matsalolin da suke damun kasar nan ko kuma ya sauka daga kan kujerarsa baki daya.

READ  FAAN Security Apprehends Intruder At MMA

“Shawara ta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ita ce, ya gane cewa ba shi ne yake da lokaci ba. Ya riga ya bata lokaci mai yawan gaske a baya. Yanzu zance ake yi na abinda zai yiwu, saboda haka yayi amfani da guntun lokacin da ya rage masa wajen kawo karshen wadannan matsaloli da kasar nan ke fuskanta.”

Leave a Reply