Duk lokacin da janaba ta samu Musulmi an wajabta masa yin wanka kafin yayi ibada na sallah ko na ‘dawafin ‘dakin Ka’abah, akwai hikimomi sosai acikin wannan wankar da shari’ar Musulunci ta wajabta, daga cikin hikimomin wankan shine rufe kofofin gashin jikin mutum da suke budewa a lokacin da maniyyi ko (sperm) yake fita a jikin mutum, gashin jikin mutum sukan bude a lokacin da maniyyi ke fita.

Budewar ‘kofofin gashin sukan sa warin jiki, wankan shi yake rufe kofofin jikin tare da hana wannan warin, idan ka lura da kyau zaka ga duk lokacin da wanda ba Musulmi ba yazo kusa da kai zaka rinka jin wani irin wari, rashin wankan janaba shi yake sabbaba musu hakan, saboda addinin su bai san da wankar ba balle su din, sannan wankan yana hana saurin kamuwa da zazzabi, idan kana yawan dadewa da janaba baka yi wanka da wuri zai rinka jawo maka zazzabi da kasala a jikin ka.

Za’a iya yin wankan a bisa tsarin ‘dayan uku, gasu kamar haka:

 1. Nana Aisha (R.A) tace “Manzon Allah ya kasance idan zai yi wanka yakan fara da wanke hannun sa (tafukan hannayen) sau uku, sai kuma ya wanke gaban sa, daga nan sai ya sake wanke hannun sa”.
  Tace “Sai kuma yayi alwala, irin alwalar da yake yi idan zai yi sallah, sai kuma ya jiqa yatsun hannun sa, sai ya mutstsuka gashin kan sa”.
READ  Sarkin Bichi: Magajin Baba inji Kanawa - Daga Usman Sarki Madobi

“Ya motsa gashin kansa da hannun sa (ba tare da ya zuba ruwa akan ba), daga nan sai ya zuba ruwa a kansa, ya wanke kan sosai sau uku, sai ya koma ya zuba ruwa a sauran sassan jikin sa, amma yakan fara wanke ‘bangaren dama, daga nan sai hagu, sai kuma ya wanke kasa har zuwa kafafun sa”.


Wannan itace cikakkiyar wankar janaba.
Karanta Sahihul Bukhariy, hadisi na 249.


“Idan ka kammala wanke gaban ka ana so ka wanke hannun ka da ‘kasa ko jikin ‘bango ko gini ko (sabulu ko omo) ko wani abinda ake amfani dashi kafin ka cigaba da wankan”.


Inji Imamun Nawawiy, acikin littafin sa “Sharhu Muslim” a Mujalladi na 3 shafi na 221.

 1. Siffa ta biyu itace; zaka fara wanke gaban ka, shike nan sai ka wanke dukkan jikin ka da ruwa, ba tare da kayi alwala ba, ba tare da ka fara wanke bangaren dama ko hagu ba, idan ka wanke jikin ka kawai da ruwa shike nan, amma dole sai kayi niyya sannan sai ka wanke gaban ka, shike nan kayi wankan.
  Idan ka so sai kayi alwala, idan kuma baka so ba shike nan sai kaje kayi sallah, wankan ya wadatar da kai ba lallai sai kayi alwala ba.
 2. Siffa ta ‘karshe itace; idan ana ruwan sama sai ka shiga cikin ruwan kawai ya wanke ka shike nan, in dai kayi niyyar wankan janaba shike nan kayi wankan janaba, ko kuma kaje ka shiga kogi ka fito shike nan, ko kuma swimming pool, idan ka fito shike nan wankan ka yayi.
  “Amma dole sai kayi niyya sannan dole sai ka game dukkan jikin ka da ruwa”.
  Karanta littafin “Al-mughniy” na Ibnu Qudamah, a Mujalladi na ‘daya shafi na 299.
READ  Dattawan Kano sun kai ƙarar Ganduje wajen Buhari

Sai kuma batun wanke baki da shaka ruwa a hanci a lokacin wankan, wasu Malamai sun ce wajibi ne, wasu sun ce ba lallai bane a sheqa ruwa ko a kurkure baki a lokacin wankan, sai dai Imamu Abu Haniyfah da Sheikh Bin Baaz da wasun su sunce wajibi ne, saboda akwai Hadisai da suka tabbatar da cewa manzon Allah ya wanke baki kuma ya shaqa ruwa a hanci a lokacin wankan janaba, dan haka kaima sai ka rinka yi.
Karanta littafin “at-ta’aliqu alal fat’hil Bariy” na Bin Baaz, a Mujalladi na ‘daya shafi na 471.

READ  An kama wani yaro da yayi yunkurin dasa bam a Coci

Wannan shine yanda ake wankan janaba, wankan haidha, wankan daukewar jinin haihuwa, shine yanda ake wankar Juma’a ko Idi, ban-bancin su kawai niyya ne.


Sai dai macen da zata yi wankan janaba ko haidha zata tsefe gashin kanta idan ruwa ba zai shiga cikin kan ba, idan kuma zai shiga shike nan ba sai ta war-ware gashin ba, sai tayi wankan da kitson akan ta.

Daga Abdul-Hadi Isah Ibrahim

Leave a Reply