Abu 3 da sarki Sanusi II ya fada a wurin taron sake fasalin tsarin iyali a Musulunci

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da uwargidansa, Aisha Buhari, mai alfarma sarkin Musulmi; Abubakar Sa'ad III, mai martaba sarkin Kano; Muhammadu Sanusi II, shugaban majalisar dattijai; Ahmed Lawan, da sauransu...

0

A ranar Alhamis ne aka gudanar da wani taro mai taken ‘sake fasalin tsarin rayuwar iyali a Musulunci domin cigaba’ a birnin tarayya, Abuja.

Taron ya samu halattar manyan shugabannin siyasa da msu rike da sarautar gargajiya mabiya addinin Musulunci daga arewaci da kudancin Najeriya.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da uwargidansa, Aisha Buhari, mai alfarma sarkin Musulmi; Abubakar Sa’ad III, mai martaba sarkin Kano; Muhammadu Sanusi II, shugaban majalisar dattijai; Ahmed Lawan, da sauransu.

READ  Babban Bankin Najeriya ta tsorata da yawan Karɓo bashin Buhari

Da yake gabatar da jawabi a wurin taron, sarki Sanusi II ya bayar da wasu shawarwari kamar haka:

  1. A kirkiri dokar da zata tilasta namiji ya fice ya bar wa matarsa da ‘ya’yansa gidansa idan aure ya mutu, watau idan ya saki matarsa.
  2. Samar da wata doka da zata hana iyaye yi wa ‘ya’yansu mata auren dole. A cewar Sarki Sanusi II, auren dole yana sahun gaba a cikin jerin matsalolin mutuwar aure, musamman a arewacin Najeriya.
  3. Kazalika, basaraken ya bayyana bukatar samun wata doka da zata ke hukunta iyayen da ke haifar yara amma su kasa sauke nauyin hakkin yaran sai dai su tura su bara, su zama almajirai. Ofishin Aisha Buhari ne ya shirya taron tare da hadin gwuiwar kwamitin koli na Muslman Najeriya (NSCIA).

Leave a Reply