Ministan sufuri ya sha da kyar a harin yan bindiga a Kaduna

Ashe yan bindigan sun yi shirin kwantan bauna ne a kan titin don haka yayin da suka hangi ayarin motocin dake tafiya sai suka bude wuta, nan da nan Sojoji da Yansanda suka mayar musu da biki aka yi ta musayar wuta...

0

Ministan harkokin sufuri a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, tsohon gwamnan jahar Ribas, Mista Rotimi Chibuike Amaechi ya sha da kyar yayin da wasu gungun yan bindiga suka kaddamar da harin mai kan uwa da wani a jahar Kaduna.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito ba ya ga Minista Amaechi, fasinjojin jirgin kasa da dama sun tsallake rijiya da baya a wannan hari da miyagu yan bindiga suka kaddamar da farmaki a kan hanyar daya hadu da tashar jirgin kasa dake unguwar Rigasa.

READ  Ganduje Installs new Emir of Kano

Lamarin ya faru ne da daren Lahadi, 16 ga watan Feburairu, kimanin karfe 8:15 jim kadan bayan jirgin ya sauke fasinjojinsa, inda wasunsu suka bi sabuwar hanyar da ta tashi daga Rigasa zuwa Mando, daga cikinsu har da ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

Ashe yan bindigan sun yi shirin kwantan bauna ne a kan titin don haka yayin da suka hangi ayarin motocin dake tafiya sai suka bude wuta, nan da nan Sojoji da Yansanda suka mayar musu da biki aka yi ta musayar wuta.

READ  Atiku son tests positive for Coronavirus

Guda daga cikin fasinjojin da harin ya rutsa dasu ya bayyana cewa: “Mun yi sa’a sosai cewa Yansanda Sojoji na kusa damu, har da ministan sufuri Amaechi a cikin fasinjojin, dan dole shi ma ministan ya koma kan hanyar Rigasa.” Inji Musa Lawan.

Da majiyar ta nemi jin ta bakin mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Kaduna, Mohammed Jalige game da lamarin, sai yace ba shi da masaniya, amma zai kara bincikawa.

READ  UNESCO donates customized Mobile Devices to Bauchi State

Sai dai cikin gaggawa, minista Amaechi ya karyata wannan rahoto, Amaechi ya yi haka ne a shafinsa na Twitter, inda yace labarun kanzon kurege ne kuma kagagge, amma bai yi bayanin abin daya faru da shi ba.

Leave a Reply