Zan sadaukar da rayuwata don samun zaman lafiya a Borno – Ahmadu Jaha

Jaha ya bayyana haka ne a zauren majalisar yayin zaman majalisar a ranar Laraba, 12 ga watan Feburairu inda yake kokawa bisa harin da yan ta’addan Boko Haram suka kai a a garin Auno wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 30...

0

Wakilin al’ummar mazabar Chibok, Damboa da Gwoza na jahar Borno a majalisar wakilai ta tarayya, Ahmadu Usman Jaha ya bayyana cewa a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa idan har hakan zai kawo zaman lafiya a yankin Arewa maso gabas.

Jaha ya bayyana haka ne a zauren majalisar yayin zaman majalisar a ranar Laraba, 12 ga watan Feburairu inda yake kokawa bisa harin da yan ta’addan Boko Haram suka kai a a garin Auno wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 30.

READ  Zulum ya yi kira ga jama’an Borno su dauki azumi a ranar Litinin don neman taimakon Allah

“Ina fadin wannan ba tare da wani tsoro ba, cewa a shirye nake na mika rayuwata idan har al’ummar dake yankin Arewa maso gabas za su samu zaman lafiya, ni na shirya sadaukar da rayuwana.

READ  Insurgents pretended to be preachers, killed 81 people, survivor tells Zullum

“Babu abin da ya fi zafi da cin rai a duniyar shi ne kana zaune cikin kwanciyar hankali yayin da al’ummar da kake wakilta suke cikin tashin hankali, ana karkashesu kamar wasu dabbobi.” Inji shi.

Jaha ya danganta harin Auno ga sakacin dakarun rundunar Sojan kasa ta Najeriya, saboda a cewarsa Sojoji sun samu labarin akwai yiwuwar samun wannan hari, amma suka yi biris ba tare da daukan wani kwakkwaran mataki ba

READ  Yanzu-yanzu: An tayar da Bam cikin Masallaci a Gwoza

Ku biyomu a Facebook: Arewa Affairs

Leave a Reply