Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Kasuwa Bakwai a Kaduna

“Yan bindigan sun isa kasuwan ne a cikin wata mota, isarsu keda wuya suka dira daga motar suka bude ma jama’a wuta ba tare da laifin fari ko na baki ba, sa’annan suka koma cikin motarsu suka arce. Amma basu dauki kayan kowa ba.” Inji shi...

0

Gungun miyagu yan bindiga sun kaddamar da harin mai kan uwa da wabi a daren Laraba, 12 ga watan Feburairu a kasuwar Maro dake cikin karamar hukumar Kajuru ta jahar Kaduna, inda suka kashe mutane bakwai.

Daily Trust ta ruwaito lamarin ya auku ne da misalin karfe 7:30 na dare yayin da yan kasuwan suke rufe shagunansu da nufin tashi, kamar yadda wani bafaden fadar Sarkin Kufana ya bayyana, inda yace baya ga kisan mutane 7, miyagun sun jikkata wasu da dama.

READ  Lack of Trust hampers Nigeria's progress- Zullum

“Yan bindigan sun isa kasuwan ne a cikin wata mota, isarsu keda wuya suka dira daga motar suka bude ma jama’a wuta ba tare da laifin fari ko na baki ba, sa’annan suka koma cikin motarsu suka arce. Amma basu dauki kayan kowa ba.” Inji shi.

READ  Photos: Kebbi State indigene invents Machine gun

Wannan hari ya faru ne bayan kwana daya da wasu miyagu suka kai hari a kauyen Bakali dake cikin yankin Fatika na karamar hukumar Giwa inda suka kashe mutane 16 yan gida daya da kuma matasan sa kai na Civilian JTF

Leave a Reply