Zan Maka Maryam Booth a Kotu – Ibrahim Deezell

"Na yarda eh, na taɓa neman ta, to amma ban taɓa 'ɗaukar ta da kyamara a ɓoye ba' a lokacin da ta ke saka kaya. Ita kaɗai ta sani, kuma ya rage nata ta kawo shaida...

0

MAWAƘIN hip-hop Ibrahim Rufa’i Balarabe, wanda aka fi sani da Deezell, ya yi barazanar cewa zai yi ƙarar Maryam Booth a kan zargin sa da ta yi na sakin bidiyon ta na tsiraici, ya na faɗin ƙarya kawai ta shara.

A cikin wata sanarwa da ya bayar a yau, Deezell ya ce idan har ba ta janye kalaman ta ba kuma ta ba shi haƙuri, to lauyoyin sa za su maka ta a kotu.

Idan kun tuna, fitacciyar jarumar ta Kannywood ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta bayar jiya cewa Deezell, wanda ta ce tsohon manemin ta ne, shi ne ya ɗauki bidiyon ta tsirara a lokacin da ta ke ƙoƙarin sa kaya.

To amma a sanarwar da ya bayar a shafukan sa na soshiyal midiya a yau, matashin mawaƙin ya ce, “A safiyar yau 09/02/2020 na karanta wata sanarwa da Maryam Booth ta wallafa a shafin ta na Twitter da sauran kafofin soshiyal midiya a ranar 8 ga Fabrairu, 2020 da ƙarfe 8:30 na dare. A ciki ta yi wasu maganganun ƙarya kamar haka:

“‘a. Ina so in tabbatar da jama’a cewa shi wannan mutum (Ibrahim Ahmad Rufa’i) ya sha yi mani barazanar cewa zai saki bidiyon idan ban ba shi kuɗi ba.

READ  Nigeria’s governance structure set up for bankruptcy , Sunusi tells

“‘…amma da gaske ne cewa Deezell tsohon manemi na ne wanda a ɓoye ya ɗauke ni hoton bidiyon a lokacin da na ke saka tufafi’.”

Deezell ya ce: “To a gaskiya ina jaddada cewa ban lamunta da wannan maganar da ke sama ba; gaba ɗayan maganar ba ta da madogara, ƙarya ce, in ban da batun cewa a da Maryam Booth budurwa ta ce.

“Ba shakka, gaba ɗayan maganar tata wani babban yunƙuri ne da aka yi saboda kishi don a ɓata mani suna, a tsinka ni a idon iyali na.”

Mawaƙin ya ci gaba da cewa, “Ina so in ƙara da cewa ban taɓa yi wa Maryam Booth ko wani mutum barazana ba don a saki wani bidiyo idan ba a ba ni kuɗi ba. Ban taɓa tambayar ita ko wani ya ba ni kuɗi ba.

“Na yarda eh, na taɓa neman ta, to amma ban taɓa ‘ɗaukar ta da kyamara a ɓoye ba’ a lokacin da ta ke saka kaya. Ita kaɗai ta sani, kuma ya rage nata ta kawo shaida.

READ  FG to disengage 200,000 N-Power beneficiaries from the scheme

“Ina nan kan baka na a maganganun da na fitar ta hanyar shafuka na na soshiyal midiya jiya ranar 08/02/2020.”

Ya kuma ce, “A tuna, a ‘yan watanni kaɗan da su ka gabata, na sha zagi da ɓatanci da kyara a intanet, wanda su waɗanda su ka aikata hakan a kai na ne kaɗai su ka san dalilin su a ci-gaba da ƙoƙarin su na sai sun karya ni na dawo daidai da matsayin su abin tausayi.

“Ban taɓa kula kowa ba a kan hakan. Kawai na ci gaba da tafiyar da rayuwa ta ne cikin jin daɗi kamar yadda na saba.

“To amma ni yanzu, a dalilin abin da ke faruwa a ‘yan awoyin nan ko kwana ɗaya, na shiga cikin babban yanayin ƙunci na ɓatanci da cin naman da ake mani ta hanyar nuna mani ƙiyayya da kyara da ƙyamata.

“Tun daga lokacin da aka wallafa maganar a soshiyal midiya, na sha samun kiran waya da saƙwanni daga iyali na da abokai na da abokan hulɗa ta, duk su na bayyana mamaki da kuma jin kunya ta a sakamakon ƙaryar da aka yi mani.

READ  Ed El-Kabir: Bauchi lawmaker, Mansur Manu disburses cash to Ward Heads, PAs

“Duk da yake da farko na tausaya mata a kan fitar bidiyon, ba zan bari ita ko wani mutum ya yi amfani da ni don cimma wani buri na ƙashin kan sa ba, ya lalata mani sunan da na yi kuma ya ƙuntata mani tare da iyali na.

“Saboda haka ina kira ga Maryam Booth da ta cire ɓatancin da ta yi mani daga dukkan shafukan soshiyal midiya ba tare da ɓata lokaci ba, sannan kuma ta ba ni haƙuri ta hanyar dukkan shafukan.

“A ƙarshe, har ma na riga na umarci lauyoyi na da su yi nazarin sanarwar ɓatancin da aka yi a kai na don su bada shawara kan matakan shari’a da ya dace mu ɗauka a kan wannan al’amari. Na gode.”

Leave a Reply