Sanatan jam’iyyar APC ya rasu a asibitin kasar Turkiyya

Sanata Longjan dan jam’iyyar APC ne, kuma ya mutu yana da shekaru 75 a duniya, shi ne mataimakin shugaban kwamitin al’adu da yawun bude ido na majalisar dattawa...

0

Sanata mai wakiltar mazabar Filato ta kudu a majalisar dattawan Najeriya Iganatius Longjan ya rasu a daren Lahadi, 9 ga watan Feburairu a wani asibiti dake kasar Turkiyya bayan fama da doguwar jinya.

Arewa Affairs ta ruwaito wani dan majalisa daya nemi a sakaya sunansa ne ya tabbatar da mutuwar abokin aikin nasa, inda yace: “Tabbas ya mutu, da safiyar nan muka gani a dandalinmu.”

READ  Yan bindiga sun kashe DPO da Insifeton yan sanda a Sokoto

Sanata Longjan dan jam’iyyar APC ne, kuma ya mutu yana da shekaru 75 a duniya, shi ne mataimakin shugaban kwamitin al’adu da yawun bude ido na majalisar dattawa.

Kafin ya zama Sanata a zaben shekarar 2019, Longjan ya taba zama mataimakin gwamnan jahar Filato daga shekarar 2011 zuwa 2015. A 2019 kuma ya maye gurbin Sanara Jeremiah Useni wanda ya tafi neman takarar gwamnan jahar Filato.

READ  Hukumar kula da kadarorin Nigeria ta kwace Gida da Kamfanin Buba Galadima

Mutuwar Sanata Longjan ta faru ne bayan watanni 2 da mutuwar wani Sanatan jam’iyyar APC daga jahar Imo, Sanata Ben Uwajumogwu.

Leave a Reply