Da Kyau Sanata Ahmad Abba Kaita – Daga lalu

Tabbas a yau a jahar mu ta Katsina APC bata karantawa wadanda sukayi wahalar siyasa ba musamman wadanda ake ganin yan tsohuwar tafiya sai gashi an wayi gari wadanda suka yaki APC da karfin su da duk wata dama da suke da ita sun zama yanlele kuma shafaffu da mai...

0

Harka da sha’ani irin na siyasa a kasar mu Nigeria aba ce mai sarkakiya da wuyar al’amari saboda yan bani na iya, fadawa da kuma yangangan da koda yaushe basa fadawa masu rike da mukamai zababbu da nadaddu gaskiya. Ta kai akwai wasu da akewa laqabi da sojojin baka wadanda babu abunda suka saka a gaba face qalubalantar duk wanda yayi suka ga gwanin su domin ayi gyara sai ayi masa ca da zagezage da baqaqen maganganu.

A dabi’ar irin yansiyasa masu bin wannan turbar har akwai masu cewa siyasa karya ce, munafunci, kisisina da kutungwila domin biyan bukatar su na gafiya ki tsira da na bakin ki kuma shugabannin sun zama ramin kura. Ta hakane da ka fadi gaskiya sai a dauke ka makiyi wanda ya daura damarar yaki da gwamnati alhali a zahiri babu babban makiyin shugaba fiye da wanda zai ga kuskure ko gazawar sa amma yayi shiru saboda tsoron hana masa ko hana masu dama ko alfarmar gwamnati.

READ  Insecurity: Katsina Govt use of Motorcycles, Tricycles

Harkar siyasa dai ta duniya ce kuma idan akwai kara to abokin daka dashi ake shan gari ayi masa gata da nono da zuma saboda nuna godiyar tayin dakar da yayi.

Hakika maganar da Mai-Girma Ahmad Babba Kaita Sanatan Katsina ta Arewa yayi game da shugabanni APC su ji tsoron Allah to gaskiya ce tsagwaronta ya fada masu domin suyi gyara.

READ  An kama wani yaro da yayi yunkurin dasa bam a Coci

Tabbas a yau a jahar mu ta Katsina APC bata karantawa wadanda sukayi wahalar siyasa ba musamman wadanda ake ganin yan tsohuwar tafiya sai gashi an wayi gari wadanda suka yaki APC da karfin su da duk wata dama da suke da ita sun zama yanlele kuma shafaffu da mai.

To amma dai abu ne na lokaci kuma, dadi na da gobe saurin zuwa. Jama’a sunyi shuru ne kawai suna jiran ranar mayar da buki domin mutanen da suka tura mota ta tashi ta bude su da kura da sannu direban motar da wadanda ya dauka zasu dawo neman agaji saboda babu makawa zata sake tsayawa irin tsayuwar cikin tsakiyar hamada da za’a sake neman masu turi, a lokacin hakorin hankali ya gama fitowa wadanda aka bude su da kura.

READ  Kisan Gilla a Arewacin Najeriya, Ina Mafita? - Usman Sarki

Duk mai son dorewar nasarar APC a zabubbuka na gaba to dole ya baiwa masu rike da madafun iko shawarar duba wadanda suka wahala da bada gudunmuwa wajen kaiwa ga nasarar jami’a.

Babu yadda zaayi ace lokacin da ludayin ku ke kan dawo ku guje mana sai kuma guri ya kure adawo mana. Ku sani dai bawan yarda yafi nasaye. Hakika Senator Ahmed Babba Kaita ya fadi abunda ke damun wahalallun APC da aka mayar bayi aka bar su da tagumi.

Ado Umar Lalu
08060306089
adumarlalu57@gmail.com

Leave a Reply