Gwamna Badaru: ka gyara tsarin shugabancinka – Daga Usman Sarki

Sai dai ga dukkan mai bibiyar abubuwa sau da kafa yasan cewa kamar lissafi na neman bace maka maimakon zage dantse sai gashi abubuwa na ja baya...

0

A cikin Jahohin Nigeria Jahar Jigawa tana daga cikin Jahohin da sukayi sa’ar samun dacen gwamnoni da sukayi dace da ke da kuduri da hangen nesa wajen ayyukan cigaba da raya kasa. A wannan fanni musanman zababbu na farar hula tun daga tsohon gwamna Mai-Girma Ali Sa’adu Birnin-Kudu duk da cewar bai dade akan mulki ba amma ya taka rawar gani. Saboda irin kokari da kwazon sa Marigayi Sheikh Lawal Kalarawi yake cewa “In Sha Allah na Kano aiki na Jigawa”.

Haka zalika Mai-Girma Saminu Turaki shima yazo da kudiri na cigaban Jahar Jigawa wajen kawo cigaban kimiyyar sadarwa, masana’antu da kuma hanyoyi. Sai dai ya gamu da babbar matsala ta rashin zama kullum yana tafiye tafiye wanda ya kawo masa cikas da nakasu akan burin sa.

Sai kuma sha kundum Mai-Girma Alhaji (Dr) Sule Lamido wanda ya shallake kowa wajen ayyukan cigaba wanda bayan irin aikin da yayi a Babban Birnin Jaha ayyukan sa sun karade duk kananan hukumomin Jahar Jigawa wanda yasa ya zama ma’aunin duk wani gwamna da za’ayi a Jigawa musanman ginin sakateriyar jaha, ginin majalissar dokoki, gidan radio, kasuwa da dai sauran su wanda har abada ba za’a taba mantawa dashi ba. Bangaren lafia da ilimi ya zama gatan marassa gata wanda ya kyautata rayuwar al’umma ta fannoni da dama.

READ  Sociology of Love and Attraction Redux 4 - By Jamilu Mukhtar

To sai ga shi cikin alfarmar Allah ka sami dama ta darewa kujerar gwamnan Jigawa. Zuwanka tabbas kowa ya shaida yadda kake da tsantseni da ririta kudin baitil malin Jigawa wanda yasa ake maka laqabi da “Baba mai kalkuleta”. Wannan kam babbar nasarace ace da kuma kyakyawar sheda.

Baya ga haka jama’a sun shaida yadda kake kula da raya yankunan karkara kana shimfida masu tituna tare da daga darajar asibitoci ta yadda kaima ka taka rawa a zangon mulkin ka na farko wajen kawowa Jigawa cigaba.

Cikin hukuncin Allah ka kai ga nasara ta lashe zabe a karo na biyu wanda wannan yasa ka wuce sabon yanka ka zama kwararren gwamna domin kasan daga inda ka fito da kuma inda zaka dosa wajen cigaba da ayyukan alheri. Sai dai ga dukkan mai bibiyar abubuwa sau da kafa yasan cewa kamar lissafi na neman bace maka maimakon zage dantse sai gashi abubuwa na ja baya. Idan muka lura da matsalar da tsohon gwamna Mai-Girma Saminu Turaki ya samu ta rashin zama to kaima zamuce tazo gareke wanda duk mai kaunar ka yasan tabbas rashin zaman ka ya karu.

READ  Kisan Gilla a Arewacin Najeriya, Ina Mafita? - Usman Sarki

Hakika mun yi tsammanin zaka cigaba da samar da masana’antu wanda Saminu Turaki ya fara a wannan zangon naka na biyu. Sai dai ana zaton wuta a makera sai gashi ta tashi a masaka. Muna ganin a matsayin ka na masanin tattalin arziqi kuma babban dankasuwa wanda ke dora kome akan sikelin muhimmanci da amfanin jama’a sai gashi ka mayar da gina masallatai a matsayin abunda kafi baiwa muhimmanci wanda mutane da dama sun baka shawara wadda kayi na’am da ita. Amma ga dukkan alamu toh ce kawai wadda hausawa ke cewa bata karya wuya.

A ganina Jigawa kamar yadda aka fada maka ginin masallatai bashi ne abunda Jigawa da ‘yan Jigawa ke bukata ba. Shawarata gare ka niyyar da kayi ta kashe wayannan makudan kudade, kamata yayi ka aje ta ka karkatar da wayannan kudade wajen lafiya da ilimi musanman baiwa haziqan ‘yan Jigawa tallafin samun karatu a ciki da wajen Nigeria wanda zasu dawo su taimaki kansu, Jigawa dama kasa baki daya.

READ  Yau a Tarihi: Kisan Sardauna, Tafawa Balewa, da abubuwa 2 da suka faru

Inayi maka tsoron batan basirar dake samun masu rike da mukaman siyasa musanman gwamnoni dasuke mayar da hankalin su akan wani abu na daban saboda basa neman zabe karo na biyu. A nawa ra’ayin zango na biyu shi ya kamata dan siyasa ya dage domin yabar tarihi abun bege.

A wannan gaba zan so kayi koyi da Mai-Girma Sule Lamido, Mai-Girma Ibrahim Shehu Shema wanda zangon su na karshe bai hana su zage dantse ba. Bugu da kari Mai-Girma Mallam Nasir El-Rufa’I da Mai-Girma Dr Abdullahi Umar Ganduje kara azama sukayi da zage dantse ba sanyi da ja baya sukayi ba.

Ina fata zaka dubi wannan shawara tawa da idon basira a matsayi na mai kaunar ka.

Usman Suleiman Sarki
sarkiusmansuleiman@gmail.com
08058330007

Leave a Reply