Barazanar Yajin Aiki – Daga Ibrahim Birnin Kudu

Wannan barazanar ta tsayar da albashi babu abunda zata tsinana face rashin fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu, wanda a karshe 'ya'yan talakawa ne zasu kwana aciki domin shi kan shi Jagoran gwamnatin, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, 'ya'yansa ba a Nigeria sukai karatu ba mafi yawancinsu, tare da sauran manyan masu fada aji a kasar nan...

0

A cikin watannin da suka shude ana samun takaddama tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’oin kasarnan, akan tsarin biyan albashin bai daya na IPPIS wanda ita ASUU ta mikawa Gwamnati bayananta wanda wannan tsari ya sabawa wasu bangarori na yadda ake gudanar da jami’o’i, amma maimakon aduba wannan matsala ayi gyara sai gashi babu abunda gwamnatin tarayya ke barazana dashi irin tsayar da albashi ga dukkan wanda bai shiga tsarin ba wanda rashin adalci ne a wannan yanayi da muke ciki.

Wannan barazanar ta tsayar da albashi babu abunda zata tsinana face rashin fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu, wanda a karshe ‘ya’yan talakawa ne zasu kwana aciki domin shi kan shi Jagoran gwamnatin, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ‘ya’yansa ba a Nigeria sukai karatu ba mafi yawancinsu, tare da sauran manyan masu fada aji a kasar nan.

Taron da Shugaban Kasa yayi tare da ministocin ilimi, kudi, sauran manyan jami’an gwamnati kowa yayi tsammani an samu maslaha, a inda Shugaban Kasa tare da goyon bayan ministan ilimi Mallam Adamu Adamu suka amince da bukatun ASUU kuma Shugaban Kasa ya bada umarnin aiwatarwa wanda suka hada harda jingine maganar tsayar da albashi a cigaba da tattaunawa domin warware wannan matsala cikin ruwan sanyi domin ganin abun bai shafi karatun dalibai ba.

READ  Miyar kuka na ƙara wa ' mata ni'ima da ƙarfin mazakuta ga maza '

Amma kash, wani abun takaici da ya kunno, kuma mayar da hannun agogo baya shine sabuwar sanarwar da ta fito daga ofishin babban Accountant na kasa a makon jiya inda ta kara jaddada matsayi da barazanar gwamnati na tsayar da albashi ga duk wanda bai shiga tsarin biyan albashi na bai daya.

Kamar yadda yan Buhariyya ke nuni cewa shi Buhari Janaral ne a soja kuma Janaral a siyasa, to ni dai na yarda Janaral ne a soja amma ba a siyasa ba. Domin indai har yakai Matsayin Janaral a siyasa babu yadda zaayi ya bada umarni domin a aiwatar da wani abu amma daga bisani a bayar da sanarwa sabanin hakan daga wani daban ba shi ba.

Wannan sanarwar ta bayyanawa mutanen Nigeria a fili maganar da Shugaban Kasa yayi na bada umarnin aiwatar da bukatun ASUU akan tsarin biyan albashi na bai daya to ba da gaske yake ba yayi fuska biyu ko magana biyu. Wanda kamar yadda yan magana ke cewa “KYAN DATTIJO MAGANA DAYA”.

READ  Mafitar Nigeria Buhari ya sauka – Sheikh Gumi

Wani abunda wannan sanarwar ta kara nuna mana shine, inhar shugaban kasa umarnin da ya bayar haka ne to ta nuna a fili kamar yadda ake zargi a kullum kuma yake musantawa cewar akwai masu juya gwamnatin shi to wannan ya fito fili a zahiri mungani. A wannan gabar duk wanda yace shugaban kasa janaral ne a siyasa to kawai yana rudan kan shi. Wallahi tallahi na tabbatar da gwaninmu Alhaji (Dr) Sule Lamido CON ne wanda shi cikakken Janaral ne mai tauraruwa hudu a siyasa ya bayar da wannan umarnin babu wanda ya isa ya sauya masa kuma idan bai gamsu da abun ba to babu tantama kai tsaye zai fadi ra’ayinsa ba tare da shakkar kowa ba kome ma zai je ya zo. Domin Lamido ya ciri tuta a tsakanin yan siyasa na tsayawa akan kaifi daya koda shi kadai ne. Bugu da kari duk gangancin manya jami’an gwamnati basa saba masa.

Kuma na tabbatar akwai sauran ‘yan siyasar da ba’a isa a sauya masu umarni ko kuma suyi fuska biyu domin wani abu ba. Amma sai ga janaral a soja cikin rigar siyasa yana fada ana sabawa ko kuma fuska biyu.

READ  Price Hike: An Advice - Ahmed Yahaya Nguru

Yan Nigeria sunyi tsammanin samun sauyin da saukin rayuwa ta dukkan fannonin kamar yadda ya rinka nunawa a lokacin yakin neman zabe. Kullum ana cewa mu kara hakuri a haka shekara hudu ta wuce ga ta biyar ta kusa har yau barazanar yajin aiki a jami’oi bata kareba.

Daga karshe, Kira na ga yan uwana yan Nigeria mugane gatan da PDP tayiwa ilimi har yau APC batayi ba, banda Kullum ganin bikin yaye dalibai na ‘yayan su a jami’o’in kasar waje ba abunda suke. Wanda ya dauke yayansa yakai Ingila ko ba’a fada ba can ya fiso ba gida ba. Da gyaran ilimin gida ake so da wannan takaddamar anyi maganin ta. Talakawa lokaci yayi da zamu damu da wadanda suka damu da mu. Allah ya wuce mana gaba ya bamu shugabanni masu kaunarmu dason cigabanmu ameen.

Ibrahim Rabiu Birnin-Kudu
Rabiu022@gmail.com
07067500700

Leave a Reply