Mata ta kona kanta saboda kishi

Matar wacce ke zaune a Unguwar Gayawa dake cikin karamar hukumar Ungogo cikin jihar Kano ta aikata wannan abu saboda tsabar kishi...

0

Tsananin kishi ya sanya wata mata ta sanyawa kanta wuta, saboda mijinta ya yo mata kishiya.

Matar wacce ke zaune a Unguwar Gayawa dake cikin karamar hukumar Ungogo cikin jihar Kano ta aikata wannan abu saboda tsabar kishi.

An bayyana cewa matar ta gama tanadar dukkanin kayan da za ta kona kan nata dasu, bayan ta gama shiri kawai ta sanyawa kanta wuta.

READ  An cafke wasu da ake zargin su da hannu a rikicin kudancin Kaduna

Matar mai suna Rabi ta kona kan nata ne bayan mijinta mai suna Badamasi ya karo mata kishiya a kwanakin baya.

A wata hira da tayi da wakilin freedom rediyo, daya daga cikin ‘yan uwan Rabi mai suna Mariya ta bayyana bakin cikinta akan wannan abu da ‘yar uwarta ta aikata akan kishi.

Haka shima wani dan uwan Badamasi mijin Rabi, mai suna Salisu Safiyanu yayi bayanin yadda wannan lamari ya faru, ya ce jikin shi ya fara rawa ne a lokacin da ya shiga gidan yaga gawar Rabi.

READ  Kiwon lafiya: Shin kun san alamomin ciwon sanyin mara ?

Har ila yau wata aminiyar Rabi da ake kira Ramatu ta nuna alhininta akan wannan mataki da kawarta ta dauka duk kuwa da cewa jami’an tsaro sun hana ta ganin gawarta.

READ  Final Crumble of Kwankwasiyya in Kano political space - By Abba Dukawa

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, wakilin freedom rediyo ya bayyana cewa ya tabbatar masa da faruwar lamarin, inda yace jami’ansu sun dauki gawar domin kai ta asibiti, domin tabbatar da tana raye ko ta mutu.

Leave a Reply