EFCC: Ku binciki Kwankwaso – Daga Usman Sarki

A tarihin siyasar Jahar Kano babu tantama tsohon Gwamna kuma tsohon Sanata Eng (Dr) Rabiu Musa Kwankwaso ya taka rawar da baza'a mantawa dashi ba wajen kawowa jihar Kano da al'ummar ta cigaba...

0

A tarihin siyasar Jahar Kano babu tantama tsohon Gwamna kuma tsohon Sanata Eng (Dr) Rabiu Musa Kwankwaso ya taka rawar da baza’a mantawa dashi ba wajen kawowa jihar Kano da al’ummar ta cigaba.

Sai dai hanzari ba gudu ba, tsohon Gwamna Kwankwaso a irin darikar siyasar sa da irin biyayyar da ake masa a wannan tafiya ta kwankwasiyya ya dauka yafi kowa tasiri a siyasance da gaskiya wajen tafiyar da gwamnati fiye da takwarorin sa tsofoffin gwamnoni.

Daya daga cikin bangarorin da tsohon Gwamna Kwankwaso yayi fice shine fanni tura yan asalin Jahar Kano karin karatu ta hanyar daukar nauyin su tare sama masu guraben karatun digiri na biyu da wanda gwamnatin sa tayi ikirarin biya. Amma sai gashi an wayi gari dalibai da dama sun shiga halin ni yasu saboda rashin biyan cikakkun kudin da ya kamata a biya masu, sai da Gwamnan Jahar Kano mai ci a yanzu Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya cika wadannan kudaden, daliban da wannan matsala ta shafa sunyi koke-koke daban daban kuma gwamnatin Ganduje ta share masu hawaye. Babban abun tambaya anan shine to ina aka kai wadannan kudaden da tsohon Gwamna yayi ikirarin ya biya amma alhali wani kaso ne ya biya ba duka ba?

READ  Tsokaci: "Gyara kayan ka....." Daga Comrade Muhammad Mobleezer katsina

Burin duk wani ma’aikaci shine ya kai matakin da zai ajiye aiki lafiya ya shiga sahun masu karbar kudin fansho. Amma sai aka wayi gari tsohon Gwamna Kwankwaso ya tattara kudaden ‘yan fansho na jihar Kano ya gina gidaje wayanda a yanzu haka irin wadannan gidajen sun fi karfin ma’aikatan Jihar Kano su mallaka saboda ‘dankaren tsadarsu. Karshe idan ba’ayi a hankali ba zasu iya zama mafaka ga marassa gaskiya da kuma aikata laifuka. Yin amfani da wadannan kudaden na yan fansho wajen wannan gine ginen ya jefa yanfanshon cikin rashin tabbas na samun fanshonsu da wahalhalu iri iri. Bisa hakan ya dace hukumar hana cin hanci, rashawa da zagon kasa ga tattalin arzikin kasa wato EFCC data binciki tsohon Gwamna Kwankwaso domin yayiwa al’ummar jihar Kano bayani filla filla kuma gamsashshe ta yadda ya karkatar da kudin ‘yanfansho a wata harkar sabanin abunda ya kamata.

READ  Zaben Kanannan Hukumomi: Gidauniyar FTS ta bukaci jam'iyun siyasa su sake mara wa matasan Gombe

Bugu da kari Mai-Girma tsohon Gwamna a muradin sa na kyautata rayuwar yan Jihar mu ta Kano mai albarka yasha alwashin gina tagwayen tituna masu tsawon kilometer biyar a kowace karamar hukuma, amma sai gashi shiru kake ji Madugu dai bai kammala su ba bayan an tattare kudaden kananan hukumomin arba’in da hudu. Anan ma muna buqatar hukumar EFCC tabi kadin yadda aka tafiyar da ayyukan wadannan tituna don sanin nawa aka cire daga asusun kowacce karamar hukuma da kuma adadin kudin da aka baiwa yan kwangila don sanin yaya aka haihu a ragaya.

READ  #RanarHausa: Bayanai akan Ranar

Har ila yau babbar gadar sama da Mataimakin Shugaban Kasa Prof Yemi Osinbajo ya kaddamar kwanannan wadda ta tashi daga Wapa har gaba da bata lokacin da Madugu yabar mulkin Jahar Kano ba’ayi nisa da aikin ba sai da Khadimul Islam ya zage dantse sannan aka kammala ta. Ya kamata yafito fili ya bayyanawa al’ummar jihar Kano tayaya yabar aikin shin kaso nawa ya biya?

Ina kira da hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa data binciki tsohon Gwamna kwankwaso a ina aka kwana.

Jihar Kano dai jihar muce kuma gyaran ta shine cigaban mu.

Usman Suleiman Sarki
sarkiusmansuleiman@gmail.com
08058330007

Leave a Reply