Dan Majalisan tarraya mai wakiltar Darazo/Ganjuwa, Hon . Mansur Manu Soro ya bayyana cewa aikin samar da ruwa a garin Soro da Darazo yayi kusan kammaluwa .

Dan Majalisan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook a yau Talata.

” Aikin mu na ruwa da muke yi a garin Soro da Darazo na mazabar Darazo/Ganjuwa ya samu kammaluwa kashi 80% cikin 100%

Nan ba da jimawa ba zamu garzaya garuruwan Kafin Madaki da Miya don fara aiwatar musu da nasu aikin kamar yanda muka shirya”.

READ  Tilde ya wallafa baitocin waka wa Matan Arewa


Ya jadda da aniyarsa na wadatar da dukkan helkwatocin gundumomi 22 dake mazabar da tsabtaccen ruwan sha.


” Manufata shine dukkan helkwatan gundumomi 22 da muke dasu a mazabata su amfana da irin wannan tsari na samar da ruwan sha mai tsafta hade da bututu mai tsawon mita 1,000 Insha Allah ”.

READ  Karan kwana: sanyi ya yi ajalin wasu abokai 2 a Jos


Ya kara da cewa ” Kamar ayyuka da muke yi na ginin asibitoci wannan aiki ma ba constituency ko capital project na Gwamnatin tarayya bane, ayyuka ne da muke yinsu da allowances din mu.

READ  Bauchi Central NYP member lauded Mansur Manu for proposing a bill for the establishment of FedPoly in Wailo

Halin da alumma ke ciki a Najeriya na murkushe kananan hukumomi da rashin sanin ina kudaden su ke tafiya tun daga shekara ta 2004 yasa dole mu sadaukar da hakkokin mu na albashi don taimakon mutanen mu doriya akan ayyukan mu na majalisa”.

Leave a Reply