Yanzu-yanzu: An tayar da Bam cikin Masallaci a Gwoza

Wani majiya daga gidan Soja, ya bayyana cewa yan kunar bakin waken sun ratsa cikin Masallaci yayinda ake cikin Sallah...

0

Yan kunar bakin wake biyu sun kai harin Bam cikin Masallaci a garin Gwoza, jihar Borno a ranar Lahadi inda yaro daya dan shekara 12 ya mutu yayinda mutane da dama suka jikkata.

READ  Hydroxychloroquine effective cure for COVID-19, says US-based Nigerian doctor

Wani majiya daga gidan Soja, ya bayyana cewa yan kunar bakin waken sun ratsa cikin Masallaci yayinda ake cikin Sallah.

Kafin Masallatan su ankara, yaun kunar bakin waken sun shige cikin Masallacin.

READ  Bauchi Govt to renovate all District Head palaces, as Wike, Bala bag traditional titles

Wannan harin ya faru ne a Guduf Nagadiyo da ke Bulabulin, Gwoza. Daga baya Sojojin bataliyan 192 suka isa wajen kuma suka yiwa Masallacin zobe.

Wani mazauni ya bayyana cewa da alamun yan kunar bakin waken sun shiga cikin garin ne ranar Asabar da aka gudanar da daurin aure a fadar sarkin Gwoza.

Leave a Reply