Zaben Kiru da Bebeji: Ku kayarda Abdulmumin Jibril – Daga Usman Suleiman Sarki

Abin takaici shine rashin sahihancin kasancewar shi wannan wakili a matsayin cikakken dan asalin yankunan Kiru da Bebeji tare da shakulacin bangaro da Wakilin ke yiwa yankunan...

0

Kasancewar wakilcin al’umma a matsayin amana, ya zama wajibi al’ummar da za’a wakilta su zabi wakili nagari mai nagarta da sanin daraja da matsalolinsu don tabbatar da isar da sakonninsu ga majalisa don samo mafita ko aiwatar da ayyukan da zasu inganta rayuwar al’umma.

A shekaru takwas da suka gabata, kananan hukumomin Kiru da Bebeji sun gamu da tsautsayi da ibtila’in wakilci a majalisar wakilai ta kasa sakamakon tsari na dauki dora da tsabar son zuciya na Gwamna a wancan lokacin.

READ  Open Letter to GOSSA National Secretariat - By Ashraf Babagana.

Abin takaici shine rashin sahihancin kasancewar shi wannan wakili a matsayin cikakken dan asalin yankunan Kiru da Bebeji tare da shakulacin bangaro da Wakilin ke yiwa yankunan.

A bisa wannan ne naga ya dace a wannan gaba nayi kira ga maqotana al’ummar Kiru da Bebeji da suyi amfani da wannan dama ta sake gudanar da zabe a wasu mazabu don kawar da Abdulmumin Jibril wanda ke a matsayin wakilin cushe tare da maye gurbinsa da Alhaji Ali Datti Yako, wanda al’umma shaida ne akan irin gwagwarmayar da yayi wajen ciyar da karamar hukumar Kiru gaba lokacin da yayi shugabancin karamar hukumar da kuma irin gudummawar daya bayar wajen gina jihar Kano lokacin da ya riqe kwamishinan kananan hukumomin jihar.

READ  Western Civilization and it's Repercussions Against African Cultures

Allah yasa ayi zabe lafiya a kare lafiya.

Usman Suleiman Sarki
sarkiusmansuleiman@gmail.com
08058330007

Leave a Reply