Bayan tabbatar da shudewar siyasar 2019 a ranar litinin data gabata 20/01/2020 yanzu abunda yake gabanmu shine yiwa Gwamnati fatan alkhairi domin cigaban jihar Bauchi.

Muna nan a jam’iyyarmu ta APC ba raba zuciya, kuma zamu amsa sunanmu na ‘yan adawa dukdacewa muma APC din gwamnati ce mai zaman kanta, amma adawa ta jahilci ne bazamiyi ba insha’Allahu, gunda akayi daidai zamu yaba kuma hakan ba yana nufin muna kwadayin shiga gwamnatin bane, haka kuma gunda akayi ba daidai ba zamu fada kuma hakan baya nufin zamiyi donmu tozarta gwamnatin ne.

Amma bazai hana in gwamnati ta tsokanemu ko wani wanda yake ganin shi QUSA ne ya tsokanemu mu barshi ba koshi wanene kuwa WALLAHI don haka ayi gwamnati mai tsafta ba tareda neman cin zarafin wani ba in anaso mu kasance masu cikakken biyayya.

READ  Abin mamaki: Aisha Buhari ta daura bidiyon Hanan cikin jirgin shugaban kasa

Sai yan APC da suke murnar an hada kai dasu an tunbuke M.A, to muma munyi alkawarin saka musu da abunda suka mana, domin suma sunyi hakane don biyan bukatun kansu kuma mun sani nan bada jimawa ba zasu fara rigima da gwamnatinda aka kawota da cikakken goyon bayansu, a wannan lokacin ne zasuzo mana da maganar hadakan jam’iya, irin wayannan mun musu tanadinda bamuyiwa gwamnatin Kaura ba, kuma zamu taya kaura fada dasu kamar yadda suka tayashi fada damu sannan muma bazamu fice a jam’iyyarba kamar yadda suma suna cikinta suka tayashi.

Sauran masu mukamai na jam’iyyar APC ‘yan amana (BAHA, REPS, SENATE) muna kira gareku da ku hade kanku ku kauracewa duk wata rigima da zata taso tsakaninku domin fidda jam’iyyar kunya, lallai mutane sun bada gudunmawa domin cimma nasararku kuma kunyi nasarar amma ga abunda ya faru da kujerar Gwamna shi kuma a bayyane take kokarinda yayi wajen kawoku wanda hakan shine yayi sanadin kara masa abokan hamayya da kusan kashi hamsin, don haka nauyi ne akanku ku kula da yaransa koda baku iya daukan dukkanin dawainiyarsu ba matukar kun duba halarcinda ya muku, ku kuma yaran Gwamna ku gane sauran kujeru bazasu iya muku abunda kujerar Gwamna zata muku ba don haka ku takaita bukatu kuma ku fara tunanin neman mafita.

READ  BVN tussles: Committee commences verification of 10,000 state, LGs pensioners today

Matsaya ta
M.A ya zama mun uba a siyansance amma yanzu Hon. Mansur Manu Soro shine alkiblata, duk gunda yasa gaba insha’Allahu muna tare, sauran masu matsayi a APC kuma (BAHA, REPS, SENATE) ina tareda duk wanda yake tare dani, amma duk wanda yake jiran wuya ta kawomu kokuma mu kawo kanmu ko muje gidansa roko kokai bukata ya wulakantamu Insha’Allahu zai tarar damu masu tsare mutuncinsu, ko a jam’iyya ana samun masu sonka da akasinsu, kamar yadda kake samun masoya a jam’iyyar da ba taka ba.

READ  Abu 3 da sarki Sanusi II ya fada a wurin taron sake fasalin tsarin iyali a Musulunci

Daga karshe ina godiyama wayanda suka jajanta mana saboda tarayya, masu zolayarmu da raha kuma Allah Ya kawo dalilinda zamu rama, masu cin mutuncinmu kuma suma Allah Ya hanasu jin dadin gwamnatin.

Maigidanmu M.A Allah ya mishi canji da abunda yafi alkhairi, shi kuma Kaura Allah Ya bashi ikon yin adalci.

1 COMMENT

  1. Kowa ya tuba don wuya ba lada. Tunaninku shine kun dauka tunda M. A. lauwaya ne ko ta halin kaka sai kun karbi wannan kujera kun manta da cewa Allah shi ke bayarwa. Sai ku koma ga Allah ku yi ta yin istigfari don don neman yafiya.

Leave a Reply