Tarihi: Shin kun san Barden Kano Idris Bayero ?

0

An haife Barden Kano, Idris Bayero a shekarar 1934,a gidan sarkin Kano , ya fara karatunsa na Elemantare a makarantar kofar kudu,san nan middle school daga nan ya halarci makarantar horon akawuna ta jami’ar Ahmadu bello dake zaria inda yai karamar diploma da babba.

Ya halarci kwasa-kwasai da dama a kan mulki,shari’a,kudade da kuma yau da kullum wato Public Administration da kuma Business Administration.

Ya fara aikin N.A. da mukamin akawu a sashen mulki(Admin) ,wanda wannan aiki ya kai shi ga mukamin sakatare a majalisar Sarkin Kano.

READ  Budaddiyar Wasika zuwa ga Aliko Dangote - Yunusa Lawan Saji


A shekarar 1976 ya rike sakataren birni (city council),bayan da aka kawo tsarin kananan hukumomi. Ya rike mukamin sakatare a kananan hukumomi jahun,Dawakin Tofa,Ringim,da kuma kaugama.Ya yi aikin banki inda ya zama akanta a bankin Arab Bank har zuwa area manager a 1981.

A shekarar 1990,Allah ya yiwa hakimin rimin gado Dan buran kano Bello Bayero rasuwa,don haka Sarkin Kano Ado Bayero ya nada shi sarautar Dandarman Kano da ba shi aikin kulawa da gundumar rimin gado.

READ  4 new emirs, Sunusi meet for the first time at Kano function

A shekarar 1992,aka ciyar dashi gaba zuwa sarautar Danburan da yi masa canjin gunduma daga Rimin Gado zuwa Bichi.

A shekarar 1996,Sarki ya ciyar dashi gaba zuwa Sarautar Barden Kano da ci gaba da zama a gundumarsa ta Bichi.

READ  Sarkin Bichi: Magajin Baba inji Kanawa - Daga Usman Sarki Madobi

Wannan aiki yake yi wanda a yanzu Mai martaba Sarkin Kano Sunusi 2 ya tabatar da shi a matsayin Hakimin Kano municipal wata cikin kwarya birni.

Wanna hoton Alh. Idris Bayero ne lokacin samartaka an dauke shi a shekara ta 1957.

Muna rokon Allah ya kara masa lafia da nisan kwana.

Daga : Kasim Tijjani Turaki da
Abdulkadir Idris Bayero.

Leave a Reply