Sarkin Bichi: Magajin Baba inji Kanawa – Daga Usman Sarki Madobi

Allah cikin ni'imarsa sai ya azurtamu da magajinsa Alhaji Aminu Ado Bayero wanda duniya ta gamsu yayi gadon dukkan kyawawan halayensa da suka zama sirrin karbuwa da daukakar marigayi sarkin Kano Alhaji (Dr.) Ado Bayero. Shine saboda halayensa na gari a lokacin mahaifinsa Kanawa sukayi masa lakabi da "Sai Kayi"...

0

Jihar Kano ta rabauta da shugaba kuma sarki mafi kima da daraja wanda yayi mulki har tsawon shekaru hamsin da daya wato marigayi mai martaba sarkin Kano Alhaji (Dr.) Ado Bayero. Alummar jihar Kano sun gamsu tare da amincewa da marigayi sarkin Kano a matsayin shugaba haziki, mai hakuri, tausayi, taimako tare da kaunar talakawansa wanda haka tasa alummar jihar Kano suke matuqar kaunarsa tare da girmamawa da martaba shi.

Marigayi ya kasance mai kokarin kare daraja da mutuncin alummarsa tare da fadakar dasu akan duk wani alamari dake da muhimmanci wajen kawo cigaba. Wannan ne yasa alummar jihar Kano ke kiransa da “Baba” saboda irin yadda yake da damuwa akan alamuransu.

READ  Shin hare-hare nawa Kiristoci su kai a wuraren Ibada?

Ranar da Allah ya karbi rayuwar sarkin Kano Alhaji (Dr.) Ado Bayero, Kano ta shiga wani yanayi na dimuwa ta rashin wannan uba wanda ya zamewa Kano, Arewa dama Nigeria garkuwa. Wannan rashi ya haifarwa da Kano wani gibi wanda keda wahalar cikewa. Muna adduar Allah ya jaddada rahama gareshi yasa aljannah ce makomarsa.

Allah cikin ni’imarsa sai ya azurtamu da magajinsa Alhaji Aminu Ado Bayero wanda duniya ta gamsu yayi gadon dukkan kyawawan halayensa da suka zama sirrin karbuwa da daukakar marigayi sarkin Kano Alhaji (Dr.) Ado Bayero. Shine saboda halayensa na gari a lokacin mahaifinsa Kanawa sukayi masa lakabi da “Sai Kayi”.

READ  Kiranyen Wakili ga Majalisar Tarayya: Kura/Madobi/Garun Malam - Daga Usman Suleiman Sarki

Alhaji Aminu Ado Bayero yana cikin manyan ya’yan marigayi sarkin Kano kuma shine ke rike da sarautar sarkin Dawakin Tsakar Gida a lokacin mulkin mahaifinsa.

Cikin hukuncin Ubangiji yau Allah ya amsa addu’ar Kanawa, Alhaji Aminu Ado Bayero shine mai martaba Sarkin Bichi kuma makwafin gurbin da mahaifinsa marigayi sarkin Kano ya bari domin a duk lokacin da tawagarsa ta shigo Kano ko ya halarci taro sai alumma su fito suna sowa tare da kuka saboda yadda yake fitowa tamkar Marigayi sarkin Kano Alhaji (Dr.) Ado Bayero da kuma yadda yake gaisawa da jama’a.

READ  Babba Kaita : Zakaran Gwajin Dafi - Daga Muhammad Mobilizer Katsina

Wannan yasa alummar Kano ke masa kirari da “Zaki Magajin Baba”.

A bisa wannan ne nake kara kira ga mai martaba sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero daya cigaba da koyi da wadannan kyawawan halaye tare cigaba da barin kofarsa a bude domin sauraron talakawa don share musu koke-kokensu.

Allah ya taimaki mai martaba Sarkin Bichi ya kara masa lafiya da tsawon zamani cikin nasara da daukaka.

Usman Suleiman Sarki Madobi
08058330007

Leave a Reply