Yau a Tarihi: Kisan Sardauna, Tafawa Balewa, da abubuwa 2 da suka faru

A ranar aka kashe Firam ministan Najeriya na farko, Abubakar Tafawa Balewa; Firimiyan Arewa, Ahmadu Bello Sardauna; ministan kudi, Festus Okotie-Eboh da Samuel Ladoke Akintola...

0

A cikin shirinmu na waiwaye adon tafiya, muna kawo muku abubuwan da suka faru masu muhimmanci a tarihin kasarmu Najeriya.

A ranar irin ta yau 15 ga watan Junairu akayi juyin mulki na farko a Najeriya.

A ranar aka kashe Firam ministan Najeriya na farko, Abubakar Tafawa Balewa; Firimiyan Arewa, Ahmadu Bello Sardauna; ministan kudi, Festus Okotie-Eboh da Samuel Ladoke Akintola.

READ  Guraben Aiki: rawar da masu rike da Mukaman Siyasa ke takawa - Daga Ado Umar Lalu

Sojoji Inyamurai sun kashe wadannan shugabannin ne domin baiwa Janar Aguiyi Ironsi daman zama shugaban kasa.

Sakamakon haka, Sojojin yan Arewa suka dau fansa inda suka kashe Sojoji Inyamurai da masu farar hula kuma hakan ya sabbaba yakin basasan 1967.

READ  Yanzu-Yanzu: Sarkin Rano Ya Rasu

Ga jerin abubuwan da suka faru:

Jan 15 1966: An yi juyin mulki na farko a Najeriya

Jan 15 1966: Kaduna Nzeogwu da Emmanuel Ifeajuna suka jagoranci juyin mulki inda suka kashe Firam Minista Tafawa Balewa da manyan jami’an gwamnati

READ  Sojojin Najeriya na Shirin kai farmaki Katsina don kakkabe 'Yan ta Adda

Jan 15 1970: Mayakan Biyafara sun mika wiya bayan shekaru biyu da rabi ana fafatawa a yakin Basasa

Leave a Reply