Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da gadojin Aminu Alhassan Dantata Flyover da ke sabon gari da kuma gadar kasa ta Tijjani Hashim da ke Kofar Ruwa.

A shafinsa na Facebook da Twitter Mai tallafawa was gwamnan akan yada labarai Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa ” Idan ba’a manta ba Gwamnatin Ganduje ta gaji gadar sabon gari a kashi 25% inda ta kara sa ta wadda aka kammala akan kudi fiye da 10Billion sannan Gwamnatin Ganduje ta kirkiro aikin gadar kasa ta Tijjani Hashim dake Kofar Ruwa domin rage yawan cinkoson ababen hawa a wurin, wadda aka gina ta akan kudi N3.5Billion” .

READ  Ganduje lauds man for trekking from Katsina to celebrate with him over victory at the Apex Court

HOTUNA: Mai Girma Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da gadojin Aminu Alhassan Dantata Flyover…

Posted by Salihu Tanko Yakasai on Monday, January 13, 2020

Haka kuma Farfesa Yemi Osinbajo ya kafa harsashin ginin sabuwar gadar sama ra Shahuci wadda kuma take hade da gadar karkashin kasa wato tunnel da zata hada asibitin Murtala da kuma bangaren Accident and Emergency domin samun saukin zirga zirga tsakanin bangarorin asibitin guda 2.

Sannan Farfesa Yemi Osinbajo ya kafa harsashin gina katafaren asibitin Cancer wanda Gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR take gina wa a asibitin Muhammadu Buhari dake giginyu, wannan shine asibitin Cancer mallakar jiha na Farko a Najeriya kuma daya daga cikin mafi inganci a nahiyar Africa ta Yamma, kuma ana sa ran Gama shi nan da shekara mai zuwa ta 2021.

READ  Senate President meets Buhari over APC crisis

Gwamna Ganduje da bakon nasa Farfesa Yemi Osinbajo sun ziyarci fadar Shugaban majalisar Sarakunan Kano Mai Martaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi II da kuma gidan tarihi na gidan Makama, inda daga nan Farfesa Yemi Osinbajo ya karasa fadar Gwamnatin jiha inda ya halarci liyafar girmamawa da aka shirya masa tare da Sarakunan Bichi, Rano, Gaya da Karaye.

READ  NYSC Corps Member Inspects self funded ongoing Construction of Maternity in Bauchi, Solicites support from Govt

Daga karshe Mataimakin Shugaban kasa ya kai ziyarar girmamawa da bangajiya, gidan Alhaji Aminu Dantata, wanda shi ma ya samu halartar kaddamar da gadar Sabon Gari wadda aka sa sunan sa.

Gwamna Ganduje ya samu rakiyar mataimakin sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna da Sakataren Gwamnatin jiha Alhaji Usman Alhaji da DG Campaign Alhaji Nasiru Aliko Koki, da Kwamishinoni da Chief of Staff Hon Ali Haruna Makoda da sauran manyan jami’an gwamnati.

Leave a Reply