Abin mamaki: Aisha Buhari ta daura bidiyon Hanan cikin jirgin shugaban kasa

Bidiyon na kusan minti daya ya nuna yadda Hanan ta yi yawon daukan hoton al'adun jihar Bauchi...

2

Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta daura bidiyon ‘yarta, Hanan Buhari, cikin jirgin shugaban kasa inda ta tafi yawon ganin ido ciki.

Bidiyon na kusan minti daya ya nuna yadda Hanan ta yi yawon daukan hoton al’adun jihar Bauchi.

READ  Photos: Turai Yar'adua visits Aisha Buhari

Hanan ta yi amfani da daya daga cikin jiragen shugaban kasa domin zuwa jihar Bauchi kuma hakan ya janyo cece-kuce inda yan Najeriya ke sukan Buhari da barin suna amfani da kudin al’umma wajen shagalinsu.

READ  Zaben Kanannan Hukumomi: Gidauniyar FTS ta bukaci jam'iyun siyasa su sake mara wa matasan Gombe

Babban lauya, Femi Falana, ya ce bai hallata ba a doka diyar shugaban kasa tayi amfani da jirgin shugaban kasa wajen harkan gabanta.

Amma duk da hakan, uwargidar shugaba Buhari, Aisha, ta daura bidiyon diyarta cikin jirgin da kuma abubuwan da taje yi jihar Bauchi.

READ  Shin da gaske ne Budurwa ta sanya samarin ta fafata zaben fidda gwani ?

2 COMMENTS

  1. To sai me ?
    Dokar kasa ce tabata ikon yin hakan, duk da cewa ana iya barin halal dan kunya,
    Amma dai idan muka kalli Gomnatocin baya ai akwai wannda Dan Minista ne ma yake daukar Jirgin Fadar Shugaban Kasa yatafi Makaranta ko wani Bukatar Kanshi Amma ba’a taba Magana ba,
    Dan Haka sai Abarta itama Lokacinta ne, idan Ubanta ya sauka daga Mulki Bata isa tayi ba.

Leave a Reply