Abin mamaki: Ashe gwamna Zulum bashi da gida mallakar kansa

Gwamna Zulum motarsa daya tak kuma bashi da gidan kansa...

1

Duk da kasancewar jiharsa ta gaba da ‘yan ta’adda suke kaiwa hare-hare tare da aiyukan ta’addanci, Gwamna Babagana Umara Zulum mutum ne mai tsananin karfin hali da kwarin guiwa.

Jajircewarsa da kuma rashin bari ‘yan ta’addan su zama babbar barazana gareshi, abin jinjina ne.

Yana zuwa ko ina a cikin jihar kuma a duk lokacin da yaso. Hatta can cikin jihar borno inda ake kallo da tsananin hatsari ko yuwuwar kai hari, gwamnan na zuwa.

READ  Nigeria confirms 4 new cases of COVID-19, as total hits 26

A cikin kwanakin nan ne gwamnan ke yawan kai ziyara asibitocin gwamnati a jihar, kuma a tsakar dare tun bayan da ya samu rahoton cewa likitoci na barin bakin aikinsu in dare yayi nisa.

READ  Nigerian Customs generates N976.6bn revenue in 8 months

Wasu likitocin kan koma gida wanda hakan ke matukar tagayyara marasa lafiya.

Gwamnan ya zage damtse wajen gina sabbin makarantu tunda sauran dake cikin jihar mayakan Boko Haram sun kone wasu kurmus.

Gwamnan, wanda aka gano dan babban malami ne, bashi da gidan kan shi kuma mota daya tak ya mallaka kafin ya zama gwamnan jihar Borno.

READ  Activist urges FG to stop dumping CSS Graduates

Ya fito daga gidan dattako kuma da kanshi yayi fafutukar da har ya kai matsayin farfesa a fannin ilimi. Yayi aiki a matsayin direban mota tasi a wasu shekarun rayuwarsa.

1 COMMENT

  1. Mun san cewa Zulium yana kishin mutanensa har da mu mazauna Maiduguri, amma menen abin yada karya akan soyayya? Don Allah ku daina rubutu akan abinda baku sani ba. Zulum yana da gidaje tun kafin ya hau gwamna ko commisioner a Borno State.

Leave a Reply