Tuni ga gwamna Ganduje – Daga Usman Sarki

Hakika wannan hanyoyi suna da matukar muhimmanci wajen inganta harkokin sufurin al'umomin kananan hukumomin Kumbotso, Madobi, Bebeji, Kiru, Karaye da Rogo kuma an fara aikin kimanin shekaru shida da suka gabata...

0

Shugabanci wani nauyi ne da Allah SWT ke dorawa akan wanda ya zaba don tafiyarda al’amuran da suka shafi al’umma. A jihar Kano gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje shine wanda Allah ya bawa ragamar shugabancin jihar Kano kuma abin sha’awa da jin dadi shine yadda gwamna Ganduje ke tafiyar da tsarin mulkinsa bisa tsarin cigaba (contuinity) domin ya zama Gwamna dake da tsarin cigaba da ayyukan daya gada daga gwamnatocin baya wanda hakan shine tsari mafi kyawu wajen tabbatuwar cigaban al’umma da alkinta dukiyar al’umma.

READ  Is there Inclusive Governance in Nigeria? - By Yusuf Kumo

A bisa wannan ne nake kira ga gwamna Ganduje daya duba tare da taimakawa wajen ganin kammaluwar aikin wasu hanyoyi guda biyu. Akwai hanyar data tashi daga Sabon titin Panshekara zuwa Madobi har zuwa kwanar Dangora sannan akwai hanyar data tashi daga Yako zuwa Karaye. Hakika wannan hanyoyi suna da matukar muhimmanci wajen inganta harkokin sufurin al’umomin kananan hukumomin Kumbotso, Madobi, Bebeji, Kiru, Karaye da Rogo kuma an fara aikin kimanin shekaru shida da suka gabata. Rashin ingancin wadannan hanyoyi yana matukar ciwa al’umomin wadannan kananan hukumomi tuwo a kwarya. A dangane da haka ne nake miqa wannan koke a madadin al’umomin wadannan kananan hukumomi don neman dauki da gudummawar mai girma gwamna Ganduje don samun kammaluwar wannan aikunan a cikin wannan shekara da muke ciki.

READ  Stop Jeopardizing Nigeria's Future - By Abba Dukawa

Allah ya taimaki gwamnatin Jihar Kano ya zama jagora garemu da shuwagabanninmu baki daya.

Daga:
Usman Suleiman Sarki Madobi
sarkiusmansuleiman@gmail.com
08058330007

Leave a Reply