Karan kwana: sanyi ya yi ajalin wasu abokai 2 a Jos

Matasan sun rasune ta hanyar nemo mafita akan sanyin dake damunsu a garin Jos...

0

Wasu matasa biyu abokan juna sun gamu da ajalinsu a kokarinsu na kauce ma radadin tsananin sanyi da ake fama da shi a garin Jos na jahar Filato, inda suka yi amfani da garwashin wuta don jin dumi, amma ya yi ajalinsu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito matasan sun hada da Saminu Idris dan shekara 25 da Idris Dahiru dan shekara 25 shi ma, dukkaninsu mazauna unguwar Gangare cikin karamar hukumar Jos ta Arewa na jahar Filato.

READ  Abin mamaki: Aisha Buhari ta daura bidiyon Hanan cikin jirgin shugaban kasa

Majiyar Arewa Affairs ta ruwaito lamarin ya auku ne da safiyar Asabar, 4 ga watan Janairu, inda matasan suka ajiye gawarshin wuta domin ya dumamasu, amma sai hayakin gawarshi ya turnuke dakin, suka dinga shakarsa a cikin barcinsu har suka mutu.

READ  Yanzu-Yanzu: Sarkin Rano Ya Rasu

Mahaifin Saminu, Malam Idris Aliyu ya tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai yace sun dauke shi a matsayin kaddara daga Ubangiji Allah, babu abin da wani mahaluki zai iya yi game da hakan, amma tabbas sun kadu matuka da mutuwar.

Daga karshe Malam Idris ya yi kira ga mazauna garin Jos dasu kiyayi kona gawarshin wuta a dakunansu da nufin shan dumi, domin a cewarsa akwasi wasu nau’o’in garwashin dake dauke da guba a tattare dasu.

READ  Ganduje Sacks Commissioner of Works and Infrastructure

Tun a ranar Juma’a ne rahotanni suka tabbatar da cewa babu garin da ta kai Jos sanyi a Najeriya, inda sanyin ya kai 6.7 a ma’aunin celcius.

Leave a Reply