Illolin Almajiranci ga al’umma-Usman Suleiman Sarki

Irin wannan halin ke jefa almajirai cikin munanan dabi'u irinsu shaye-shaye, ta'addanci, sata, daba da barandar siyasa wanda hakan ba karamar barazana bace ga....

0

Almajiranci wata dabi’a ce da ta zamo ruwan dare a arewacin Nigeria.

Wasu mutane cikin al’umma sun dauki almajiranci a matsayin hanya daya tilo da ya’yansu zasu samu karatun Al’qurani mai tsarki duk da cewa akwai makarantun islamiyyu da ake bayarda ilimin Al’qurani, Hadisi da fiqhu wadanda sai dasu ibada da addini ke inganta.

Tsarin almajiranci a wannan zamani yasha ban ban da irin yadda yake a baya duba da yadda ake barin almajirai kara zube babu kyakykyawar kulawa daga iyaye da malamansu wanda hakan ke jefa wasunsu cikin munanan halin rashin da’a da tarbiyya dabe dace da addinin musulunci ba.

Abune bayyane karara yadda almajirai ke yawo a tituna da kasuwanni da nufin neman abincin da zasu ci ko kudin da zasu sayi wasu abubuwa da suka zama wajibi a harkar rayuwa kamar su sabulun wanka, wanki, takalmi da magani yayin rashin lafiya.

READ  Shugabancin Buhari Yafi Cutar Corona Illa ga Al'ummar Najeriya- Daga Sarki

A kokarin neman wadannan abubuwane wasu almajiran ke fadawa hannun bata gari wanda suke chanza musu tunani da tarbiyya inda daga bisani suke zama matsala ga malamansu, iyayensu harma da al’umma baki daya.

Sanin kowa ne tarbiyyar yara bata inganta sai da kulawar iyaye da malamai amma abin takaici shine yadda wasu iyaye da malamai ke rikon sakainar kashi ga ya’yansu ko dalibansu ta hanyar kula tare da bibiyar halin da yaransu ke ciki don tabbatar da cewa suna karatu kamar yadda ya kamata kuma basa mu’amala da gurbatattun mutane.

READ  Nigeria's Democratic Backsliding- By Aminu Ali

Bugu da kari iyayen a wannan zamani suna kai ya’yansu makarantun Allo don almajiranci ba tare da sun samar musu da abinci ko sabulun wanka da wanki ba sannan basa kai ziyara a makarantun don tantance yanayin da ya’yan nasu ke ciki tare da sauraron matsalolinsu.

Irin wannan halin ke jefa almajirai cikin munanan dabi’u irinsu shaye-shaye, ta’addanci, sata, daba da barandar siyasa wanda hakan ba karamar barazana bace ga tsaron al’umma. Haka kuma wannan rashin kulawa ke janyo rashin tausayi da jin kan iyaye daga almajiran da suka fuskanci irin wannan rashin kulawa.

READ  Soleimani Killing: Shiites Protest In Abuja, Burn US Flag

A bisa wannan nakeso inyi amfani da wannan dama wajen tunatar da iyaye irin nauyin dake kanmu na bayar da ingantacciyar tarbiyya ga ya’yanmu don samun al’umma tsaftatacciya tare da kyautata alaqa tsakaninmu da ya’yanmu. A karshe nake mai shawartar hukumomi da sarakunan gargajiya da masu hannu da shuni da su samar da wata kafa da za’a tattara shawarwarin al’umma don samo mafita ga wannan al’amari.

Allah ya taimakemu ya taimaki al’ummarmu baki daya.

Usman Suleiman Sarki Madobi sarkiusmansuleiman@gmail.com
08058330007

Leave a Reply