Sanin kowane tsaro shine ginshiqin cigaban kowacce irin al’umma domin sai da tsaro ake samun nutsuwa da kwanciyar hankalin gudanar da duk wani al’amari da zai kawo cigaban al’umma.

A tarihin Nigeria musamman kasar hausa, sarakunan gargajiya sun taka muhimmiyar rawa wajen kyautatawa da tabbatar da tsaron al’umma ta hanyoyi da dama. A tsari irin na sarautar gargajiya, Sarakuna na kokari wajen kula da shige da ficen al’umma musamman baqi domin tabbatar da sahihancin baqin dake shigowa don kaucewa ajiye bata gari da ka iya haifar da matsalar da zata shafi tsaron al’umma.

READ  Daren farko shin me ma'aurata ya kamata su sani ?

Sarakuna a matsayin iyayen kasa suke tabbatar da bin doka da oda ta hannun Hakimansu, Dagatai da masu Unguwanni kasancewarsu kusa da al’umma. Suna aiwatar da wannan ayyuka ne ta hanyar fadakarwa, tunatarwa tare da tsawatarwa. Wannan ce tasa suka zama ababan dogaro wajen harkokin tsaro kuma suka samu mazauni a majalisar tsaro a matakai daban daban na gwamnati. Bugu da kari Sarakuna sune suke tallafawa jami’an tsaro wajen zakulowa ko nemo ingantattun bayanai dake da nasaba da masu aikata miyagun laifuka don tabbatar da cewa an musu hukunci daya dace saboda ya zamo darasi garesu dama duk mai niyyar aikata laifi.

READ  Kiranyen Wakili ga Majalisar Tarayya: Kura/Madobi/Garun Malam - Daga Usman Suleiman Sarki

A bisa wannan ne ya zame mana wajibi muyiwa Allah godiya bisa azurtamu da Karin masarautu da Sarakuna masu daraja ta daya wanda zasu taimaka wajen tabbatuwa da ingacin tsaro a Jihar Kano tare da tabbatar da samun cigaba ta dukkan fannonin rayuwa na yau da kullum musamman harkar ilimi, lafiya, noma da al’amuran kasuwanci.

READ  Budaddariyar Wasika zuwa ga Ministan Sadarwa, Pantami

A karshe muna addu’ar Allah SWT ya karfafi Sarakunan nan namu wajen jajircewa ta fannin kulawa da al’ummominsu ya kara daukaka dukkan masarautunmu baki daya.

Usman Suleiman Sarki Madobi
sarkiusmansuleiman@gmail.com
08058330007

Leave a Reply