Kira ga Sarkin Bichi – Daga Usman Sarki Madobi

inaso inyi amfani da wannan dama domin neman alfarmar Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero daya duba tare da amincewar majalisar masarautar Bichi domin nada Mai Girma Gwamna Ganduje a matsayin SARDAUNAN BICHI....

0

Yana daga cikin kyawawan halaye na karamci da kyautatawa shugaba ya zama mai kulawa da bukatun al’ummar da yake shugabanta tare da bijiro duk wani al’amari dazai inganta rayuwarsu tare da tabbatar da zaman lafiya da kyautata al’adun al’umma.

Tsayawa bisa wadannan halaye ne da mai girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi ne yasa ya zamto zakaran gwajin dafi wajen kula da bukatun al’ummarsa. Al’umma shaida ne na irin yadda Gwamna Ganduje ya jajirce wajen kammala ayyukan daya gada a wajen gwamnatocin da suka gabata har saida ya kammala kuma daga bisani ya fara aiwatar da nasa ayyukan wanda gwamnatin Ganduje ce ta farko a tarihin Kano ta zamo mai kammala ayyukan wasu gwamnatocin da suka wuce.

READ  Matasa Sune Mafi Dacewa da Jan Ragamar Shugabanci a Najeriya - Daga Usman Sarki

Bugu da kari, Gwamna Ganduje ya kawo ingantaccen tsarin bayar da ilimi kyauta tare da samar da kayayyakin aiki a makaratu mallakar gwamnatin jihar Kano, samarda uniform kyauta ga daliban makarantun firamare mallakar gwamnatin jihar Kano, kammala gadoji da tituna a kofar ruwa, Fagge, sabon titi da zoo road a cikin birnin Kano. Bai tsaya nan ba Gwamna Ganduje ya daukin nauyin horarwa tare da samar da jari ga matasa a kokarinsa na rage rashin aikin yi a tsakanin matasa. Haka zalika gwamnan ya kara martaba hukumomin Hisba da Karota tare da sama musu kayayyakin aiki don tabbatar bin dokokin musulunci dana tuki a fadin jihar Kano. Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Ganduje ta amince da Gina sabbin manyan asibitoci a dukkan masarautu guda biyar dake jihar kano don inganta harkar lafiya.
A kokarinsa na kara matso da talaka kusa da gwamnati, Gwamna Ganduje ya sanya hannu tare da aiwatar da dokar kara kirkiro masarautu masu daraja ta daya guda hudu wanda suka hada da Bichi, Gaya, Karaye da Rano domin kusanto da talaka ga gwamnati ta hannun sarakuna a matsayinsu na iyayen kasa. Koda a kunshin kwamishinoninsa, Gwamna Ganduje ya tabbatar da adalci wajen zabosu daga dukkan wadannan masarautu namu guda biyar wanda a baya babu cikakken wakilcin dukkan bangarori musamman kananan hukumomin dake wajen Kano.

READ  Siyasar Jihar Katsina: Riba ko faduwar dimokradiyya ?

A bisa karamci da duba bukatunmu, mu al’ummar jihar Kano tare da amsa bukatarmu ta kirkiro sabbin masarautu da Sarakuna masu daraja ta daya, inaso inyi amfani da wannan dama domin neman alfarmar Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero daya duba tare da amincewar majalisar masarautar Bichi don nada Mai Girma Gwamna Ganduje a matsayin SARDAUNAN BICHI duba da kasancewarsa mai kokari wajen hidimtawa al’umma a koda yaushe.

READ  Raba Kayan Abinci Daga Ministan Abuja
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje

A karshe ina Adduar Allah ya taimaki jihar Kano ya kara mana lafiya da zama lafiya.

Usman Suleiman Sarki Madobi
sarkiusmansuleiman@gmail.com
08058330007

Leave a Reply