Shehu ya shiga cikin kundin tarihin duniya

Shehu ne mutum guda a tarihin Duniya daya tattara jimillar zuri'a har mutum 601, dukkaninsu sun gogu a harkar ilimin Islama dana Boko....

0

Fitaccen malamin darikar Tijjaniyyah, Shehu Dahiru Usman Bauchi ya shiga cikin jerin mutanen da gidauniyar “CHOLAN BOOK OF WORLD RECORD” ta karrama da lambar yabo na kafa tarihin da ba’a taba samunsa ba a Duniya.

Gidauniyar ta karrama shehin Malamin ne bisa wasu tarihi guda 7 daya kafa a matsayinsa na mahaddacin Al-Qur’ani mai tarin iyali, inda tace ta tabbatar da haka ne bayan doguwar nazari da tantancewa da ta gudanar.

READ  Siyasar 2019 ta kare : Ina muka dosa ? - Daga Yusuf Burku
Shehu Dahiru Uman Bauchi

Wannan kungiya ce da take da burin yin aiki domin bayar da gudummowa ta fuskar habbaka ilimi, samar da horo akan harkokin da suka shafi al’adu da kuma fayyace wadanda suka cimma gagarumar nasara a rayuwar su, a wannan takarda da ta kunshi tarihin fitattu a Duniya.

READ  Shin wa zai zama sabon Sarkin Rano ?

A cewar gidauniyar “Cholan Book Of World Record” Dahiru Bauchi ne mutum guda a tarihin Duniya, da ya tattara jimillar iyalai (Zuri’a) har mutum 601 , dukkaninsu sun gogu a harkar ilimin Islama dana Boko, wadanda suka kunshi;

– ‘Ya’ya 95

– Jikoki 406

– Tattaba kunne 100

– Yaransa 77 mahaddata Al-Qur’ani ne

READ  Daren farko shin me ma'aurata ya kamata su sani ?

– Jikoki 199 mahaddata Al-Qur’ani ne

– Tattaba kunne 12 mahaddata Al-Qur’ani ne

– Shehi, mahaifinsa da Kakansa duk mahaddata Alkur’ani ne

Da wadannan bayanai ne gidauniyar “Cholan Book Of World Record” ta tabbatar da cewa babu wanda ya taba samar da wannan tarihi abin al’ajabi a fannin ilimi a duniya gaba daya.

Leave a Reply