Wata sabuwa daga mazabar Kura/Madobi/Garun Malam, akwai alamar tambaya akan ingancin kasancewar wakilinmu na majalisar tarayya cikakken dan asalin jihar Kano.

A kokarinmu na bibiyar ayyukan raya kasa da wakilinmu a Majalisar Tarayya ya aiwatar kamar yadda ya ambata yayi a yankunan kananan hukumomin Kura, Madobi da Garun Malam, alamu sun fara nuni da rashin tabbacin kasancewar wakilin dan asalin Jihar Kano.

Wata ruwaya ta bayyana mana cewa wakilin dan asalin wata Jiha ne a jihohin arewa maso gabas sai dai ya zauna a wannan jiha ne kuma ya samu damar shiga siyasa ta iyayen gida wadanda sune ummul aba’isin tsayar dashi takara don wakilcin wadannan yankuna namu.

A halin yanzu kwamitinmu na bibiyar ayyukan raya kasa da wannan Wakili ya labarta ya aiwatar ya duqufa wajen tattaro dukkan bayanai don tabbatar da gaskiya da sahihancin wannan al’amari domin daukar mataki na gaba.

Muna Kara kira ga wakilai na wannan kwamiti wadanda suka fito daga kananan hukumomin Kura, Madobi da Garun Malam dasu cigaba da jajircewa don tabbatar da nasarar wannan aiki.

A karshe muna kara godiya ga al’umomin yankunan kananan hukumomin Kura, Madobi da Garun Malam bisa hadin kai da goyon baya da suke bamu.

Usman Suleiman Sarki Madobi. 08035323230

READ  Guraben Aiki: rawar da masu rike da Mukaman Siyasa ke takawa - Daga Ado Umar Lalu

Leave a Reply