Kiranyen Wakili ga Majalisar Tarayya: Kura/Madobi/Garun Malam – Daga Usman Suleiman Sarki

Duba da rikon sakainar kashin da dan mjalisarmu yake mana, ya zama dole mu tashi tsaye....

0

Kananan hukumomin Kura, Madobi da Garun Malam kananan hukumomi ne dake da wakili daya a Majalisar tarayya wanda ke da alhakin gabatar da kudurori da buqatun al’umomin wadannan yankuna don kawo cigaba mai dorewa a yankunan.

Sai dai abin takaici shine yadda wadannan yankuna ke fama da rashin halattacce Kuma ingantaccen wakilcin sakamakon tsautsayin tura wakilin da bashida masaniyar halin da al’umomin wadannan yankuna ke ciki kasancewarsa bako a yankunan duk dayake dan asalin wannan yanki ne amma mazauni a wajen yankin.

Bugu da kari wannan wakili bashida wani lokaci dayake ziyartar wadannan yankuna don jin halin da al’umomin yankunan ke ciki wanda hakan wata alama ce dake nuna rashin damuwa da al’umomin da aka taka gadon bayansu aka kai inda ake a yanzu.

READ  Shin kun san yadda ake wankan tsarki ?

To amma ba anan gizo ke saka ba domin akan samu yan siyasa wadanda ba mazauna yankunansu na asali ba amma kishin al’umma yasa suna lura da buqatun al’umominsu tare da sauke nauyin da Allah ya dora musu.

Misalin Honourable (Dr.) Musa Iliyasu Kwankwaso dan siyasa ne wanda ya fito daga karamar hukumata ta Madobi kuma yana zaune ne acikin birnin Kano amma a matsayinsa na dan siyasa ya jajirce wajen taimakawa yankin karamar hukumarsa kuma bashida abokan siyasar da suka fi yan karamar hukumarsa.

READ  Tarihi: Shin kun san Barden Kano Idris Bayero ?

Al’ummar karamar hukumar Madobi shaida ne akan irin gudummawar da Honourable Musa Iliyasu Kwankwaso yake bawa karamar hukumar Madobi.

Duba da irin rikon sakainar kashi da wakilinmu a Majalisar tarayya kewa wakilcinmu, ya zama wajibi al’ummar wadannan kananan hukumomi na Kura, Madobi da Garun Malam mu tashi tsaye don yin amfani da damar da dokar kasa ta bamu na sauya duk wani zababbe ta hanyar da doka tayi tanadi don tura mutumin da muke ganin zai gabatar da Wakilci nagari a wannan majalisa ta hanyar gabatar da buqatun al’ummar dayake wakilta tare da samar da ayyukan yi ga matasa, bawa mata jari don dogaro dakai tare da tallafawa matasa wajen karatu a matakai daban daban.

READ  Broader Conception of Security Situations in Nigeria - By Ahmad Muktar Saleh

A karshe ina kira ga al’umomin yankunan Kananan hukumomin Kura, Madobi da Garun Malam da mu farga don samar da Wakilci nagari domin al’ummar wadannan yankuna namu su fara amfana da ayyukan cigaba kamar yadda muke gani a makwabtanmu.

Usman Suleiman Sarki
sarkiusmansuleiman@gmail.com

Leave a Reply