Guraben Aiki: rawar da masu rike da Mukaman Siyasa ke takawa – Daga Ado Umar Lalu

A yananin da ake ciki sau tari za mu ga an saka talla ko shellar daukar aiki ta gidajen radio, talabijin, jaridu da sauran kafafen yada labarai.

0

Samun guraben aiki a kasar mu Nijeriya abu ne mai matukar wahala musamman ga talakawa wadanda basu da kowa kuma basu san kowa ba.

A yananin da ake ciki sau tari za mu ga an saka talla ko shellar daukar aiki ta gidajen radio, talabijin, jaridu da sauran kafafen yada labarai. Amma mafi yawan lokutta irin wadannan tallace-tallacen ana yinsu ne kawai domin cikon umarnin amma ana raba guraben ga masu uwa a gidin murhu ta hannu iyayen gidan su. A irin wannan yanayi sai sa’a ka ga wanda bashi da kowa bashi da komai ka ga ya samu.

Amma duk da haka masu rike da mukaman siyasa zababbu da nadaddu suna taka muhimmiyar rawa wajen samawa matasa ayyukan yi tun daga matakin kananan hukumomi, jahohi da kuma gwamnatin tarayya.

Wannan yana samuwa ne saboda damar da yan siyasa ke da ita a lokacin da suke da dama kafin damar ta wuce. A duk mazabu da muke dasu tun daga matakin Ward, Karamar hukuma, mazabar dan majalissar jaha, mazabar dan majalissar tarayya, mazabar sanata, gwamna da shugaban kasa za mu ga cewar kujeru ne da suka zama kujerun aski sai da wasu suka sauka sannan wayansu suka hau wanda ke nuna mana cewar babu mai dawwama akanta kome daren dadewa sai an wayi gari wasu ke bada umarni a wurin da a bayan ku ne ke badawa, kuma kune ake so a gani yanzu kuma tarihi yawuce da ku.

READ  Da Kyau Sanata Ahmad Abba Kaita - Daga lalu

Tunda mulki ba ya dawwama ga masu zurfin tunani da hangen nesa, sukanyi amfani da wannan damar kafin ta kubuce su yi ayyukan rawa kasa da za su kawo ci gaban al’umma wanda zaa rinka tunawa dasu bayan tsawon zamani kamar su kyautatawa da inganta harkokin ilimi, kiwon lafia, samar da ruwan sha, tituna da kuma habakar tattalin arziqi domin yaki da talauci wanda zai inganta rayuwar al’umma.

Baya ga wayannan abubuwan da na lissafa a sama, wata dama da masu rike da mukaman siyasa suke da ita zababbun su da kuma nadaddun su shi ne samawa jama’ar su ayyukan yi a matakai daban-daban domin sama masu abubuwan dogaro da kai da zasu taimaki kan su, iyayen su, makwabta da kuma al’umma baki daya. Duk wanda ka taimaka masa yasamu aikin yi to tabbas kayi masa wani tanadi ne na rayuwa inda har kullum duk abunda ya samu kuma yayi aiki dashi kana da lada.

READ  Budaddariyar Wasika zuwa ga Ministan Sadarwa, Pantami

Yan siyasa a wasu wurare suna da tsari na kokarin sakawa mutanen mazabunsu domin nuna godiya da ya bawa ga wadanda suka yi masu wahalhalun siyasa sannan kuma sauran jama’a gwargwadon hali.

A shekara ta dubu biyu da sha daya (2011), mun yi magana da wani makusanci dan majalissar tarayya a wata mazaba ta Kano, na ce masa me ya sa Mai-gidansu baya samowa mutane aikin yi musamman wadanda suka yi masa wahala. A karshe wanda ya gaje shi a wannan kujera har laqabi ake masa da “mai-gonar offer”. Bayan shi, Hon. Farouk Lawan ya taimakawa yan mazabar sa har da sauran sassan Kano da samun ayyukan yi da a yanzu haka wayansu su sun shiga cikin manyan maaikata. Ina da misalai da yawa a Jahar mu ta Katsina, Kano, Jigawa, Bauchi, Kaduna da sauran su na irin kokarin da masu rike da mukaman siyasa wajen samawa jama’ar su aikin yi.

READ  Tsokaci: "Gyara kayan ka....." Daga Comrade Muhammad Mobleezer katsina

Irin wannan kokari na yan siyasa yana sama masu tagomashi da kima a idon jama’ar su har da sauran mutane wayanda suka amfana dama wayanda basu amfana ba, saboda shi abun alheri ko ba kai aka yi wa ba idan kaji labari za ka ji dadin sa sosai. Saboda wannan zainuna yadda suke so da kuma kaunar jamaar su da zai sa ko bayan basa nan za su zama abun misali a cikin al’umma.

Ina so in yi amfani da wannan dama ga dukkan masu rike da mukaman siyasa (Nadaddu/Zababbu) da su yi hobbasa wajen zama gatan marassa gata daga cikin mazabun su kamar yadda yan-magana ke cewa “saboda towon gobe ake wanke tukunya”, kuma “idan kana da kyau ka kara da wanka har ka saka da turare”.

Ina rokon duk wadanda suka yi nisa cikin wannan kokari to su kara zage dantse, ga wadanda basu fara ba to su yi kokari domin lokaci ake sallata.
Allah ya taimaki mai taimako.

Ado Umar Lalu
adoumarlalu57@gmail.com
08060306089

Leave a Reply