Dan Majalisan wakilai mai wakiltar mazabar Darazo/Ganjuwa, Hon Mansur Manu Soro ya shirya tsab don mika ginannen karamar asibiti a kauyen Shila cikin karamar Hukumar Ganjuwa.

Mansur ya bayyana hakannen a shafinsa na Facebook.


Yace ” A farkon shekaran nan ta 2019 na fara aikin gina asibitin haihuwa a garin Shila dake karamar hukumar Ganjuwa.
Hakan ya faru ne saboda koke da shugabannin wannan yanki da suka kunshi kauyuka sama da 15 suka kawo mun cewa rashin maternity ya jawo asarar matansu masu haihuwa sama da 10 cikin shekara daya. ”

READ  Da Kyau Sanata Ahmad Abba Kaita - Daga lalu

Ya bayyana cewa kayyayakin asibiti har ya kammalla sayan su.

” Yau cikin ikon Allah na samu daman sayan kayan asibitin bayan kammala aikin ginin. Har ila yau na rubuta takarda zuwa ma’aikatar kula da kiwon lafiya daga tushe don ta tura kwararriya zuwa ga wannan asibitin don soma aiki”.

READ  Shin da gaske ne Budurwa ta sanya samarin ta fafata zaben fidda gwani ?

Danmajalisan ya kara da cewa a yau Talata 17 ga watan Disamba ne zai mika asibiti da kayan aikin wa al’umomin yanki.

” Gobe zan aika da komiti da zasu kai wannan kaya zuwa garin Shila don su damka shi a hannun komiti da wadannan kauyuka zasu kafa don kula da asibitin.
Insha Allah zan cigaba da daukan dukkan matakai wajen sadaukar da kadan da nake samu don tabbatar da walwalar al’umman da nake wakilta ”

READ  Mansur Manu Soro: One year of uncommon representation - By Kaluri Ayuba

Leave a Reply