Baiwa daga Allah, Wani matashi ya kware wajen zane-zane

0
60

Daga Ismail Idris Abdullahi

Wani matashi dan asalin Jihar Bauchi , Hussain  Tilde  Ta karamar Hukumar Toro a garin Tilde, ya kwarace wajen zayyana da zane-zane abubuwa masu kayatarwa.

Shi dai wannan matashin mazaunin garin Gombe yayi karatunshi a jiharshi Bauchi amma yana aikine agarin Gombe wanda hakan nema ya tilatashi yasa yatashi yashirya tsaf danganin yanemawa kansa da matasan Arewa madogara tahanyan yin amfani da baiwar da Allah yamasa na zane da ‘creative arts‘ abundai sai kagani.

Matashin dai yafara buga-buga dan ganin yasamu jari dan fara wannan sana’a nashi na zane cikin ikon Allah yasamu abunda yasamu kuma yafara sana’arshi abun dai sai kagani kawai gashi matashin yafara dakafar dama dan yasamu karbuwa kuma yana amfani dakaya masu inganci sosai.

Ganin yanda matashin yake fadi tashi danganin yasamu kanyan dogaro dakanshi yasa nayi sha’awar zantawa dashi kuma nasamu nasaran jin ta bakin sa sai dai kuma ya sanar da mu wani babban kalubale wanda yake fuskanta kusan shine yake saka yawancin matasa suke baya baya da sana’a irin wannan.

“Na farko ba wadataccen jari  inda kayan aikin  namu suna da tsada sosai wanda sai kagama aikinka sai kaga mutanenmu da ya kamata su  taimaka maka amma sai kaga suna neman karyaka, Basai nayi wani dogon bayaniba nasan kowa yasan halin mutanenmu” inji Hussaini Tilde.

Ya kara da cewa ”Daga karshe dai danyi amfani dawannan dama dan jan hankalin yan kasuwanmu, yan siyasa da masu fada aji dasuyima Allah suna tallafa wa  matasa da jari da  kuma kokarin sayan kayan dasuke kerawa dan hakanne dai karama matasa karfin guiwa dan nemawa kansu mafita”.

Ga saura zane-zanensa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here