Aure Ibada ne ba gasa ba – Amina Mubarak

0
5
Matashiya mai fafutukar kare hakkin mata kuma kodinetan One Campaign a Jihar Bauchi ta rubuta sharhi akan yadda aure ya zama al’ada a kasar Hausa…
A yanda muka samu ukanmu yau mafiya yawan aurarraki da akeyi basu da alkibla sannan mafiya yawan ma’urautan basu san auren a addinance ba saboda haka basu san hukunce hukuncen addini ba dangane da auren ba. Miji bai san hakkokinsa akan mata ba itama mata batasan hakkokinta akan miji ba.
A yau an maida aure al’ada ne ba ibada saboda kawai nataso nagirma naga Baba na yana auren Mama na sannan in mutum yakai wani mataki na shekaru a rayuwarsa in bukatar aure ya taso masa sai yayi aure inda wasu daga cikinsu basusan ma yadda zasuyi wankan tsarki ba not to talk of sauran abubuwa. 
Yarinyace bata masan hukunce hukunce dangane da al’ada ba uba zai aurar da ita batare da tasan auren ba a addinance kawai dai ita an aurar da ita zataje ta zauna gidan miji kamar yadda taga matan garinsu su nayi. 
Mun sani cewa aure sunna ne na fiyayyen Ma aiki Annabi Muhammad ( SWA )amma dayawan wadanda sukayi aure yau basusan Tarihin Annabi da matansa ba, tarihin yadda yayi rayuwa da matansa da yadda ya muamalncesu ba. Amma zaku  bugi kirji kuce raya sunna Manzo SWA kukeyi bayan bakusan Sunnah dinba.
Uba kafin ka aurar da yarka ka tambayi kanka me kasanar da yarka game da aure, wani ilimi na addini ka bata da zai zama jagorarta a rayuwar aurenta? 
Yayanku kiwo ne da Allah yabaku kuma sai ya tambayeku akan wannan kiwo da yabaku.
Aure ibada ne ba kawai jin dadi ba.
Aure fa ya wuce yin jima’i da tara tulin ‘ya ‘ya ba
Muyi wa kanmu karatun ta nutsu mu kuma tambayi kanmu.
Kar Garin neman lada a samu sabanin haka.
Amina Mubarak Ahmad, Bauchi State One Campaign Coordinator and SDGs Youth Network

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here